Da safiyar Laraba mutane da dama sun razana yayin da gobara ta kama a daya daga cikin rassa na bankin Access daura da hanyar Ademola Adetokunbo da ke gundumar Victoria Island a kwaryar birnin Legas.
Aukuwar musibar ta tashii hankulan mutane da dama da ke makwabtaka da ginin bankin da kuma sauran ofisoshi a yankin da ake hada-hada ta harkokin kasuwanci.
Majiyar mu ta fahimci cewa, gobarar ta tashi ne a yayin da wata tanka da ke kokarin sauke dakon makamashi na iskar gas a wani Janareta da ke harabar bankin.
Jami’an kwana-kwana da kuma Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Jihar Legas (LASEMA), sun yi iyaka bakin kokarinsu wajen kashe wutar.
Darekta Janar na LASEMA, Olufemi Oke-Osanyitolu, ya tabbatar da faruwar hakan da cewa an yi gagarumar sa’a yayin da babu ko ran mutum daya da ya salwanta.