Wata gobara ta tashi da sanyin safiyar Talata a babbar kasuwar Sakkwato.
Gobarar wacce ta tashi da misalin karfe 7:00 na safiya na can na ci gaba da ci har zuwa lokacin hada wannan rahoton.
- Shugaban karamar hukuma ya rasu kwanaki 3 bayan lashe zabe a Kano
- Matar aure a Kano ta kashe budurwar da mijinta zai aura
Rahotanni dai sun nuna cewa wani injin janareta ne ake zargin ya haddasa gobarar.
“Wutar ta fara tashi ne daga jikin wani janareta a Kofar Yan Roba,” inji wani jami”in kashe gobara.
Wakilinmu ya ga ma”aikatan Hukumar Kashe Gobara ta Kasa da na Jihar ta Sakkwato suna ta kokarin kashe wutar.
Kawo yanzu dai ba a kai ga tantance iya barnar da gobarar ta yi ba, ko da yake tana ci gaba da kone dukiyoyi na miliyoyin Naira amma ba a sami asarar rai a cikin ta ba.