✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobara ta lalata bangaren kasuwar Katsina

A ranar Litinin da ta gabata ne gobarar da ta tashi a cikin dare a babbar kasuwar Katsina ta kona wasu shaguna, inda aka yi…

A ranar Litinin da ta gabata ne gobarar da ta tashi a cikin dare a babbar kasuwar Katsina ta kona wasu shaguna, inda aka yi asarar dukiya mai dimbin yawa.

Gobarar ta shafi rukunin wasu shaguna ne da ke yankin da ake kira na wucin-gadi.
Bayanai sun ce abubuwan da gobarar ta lalata sun hada da gwala-gwalai, da tufafi da kuma wayoyin salula da miliyoyin naira.
Rahotanni sun ce wutar ta yi kusan sa’a uku tana ci kafin a shawo kanta.
Wani wanda abin ya faru akan idonsa ya ce: “Wutar ta fara daga wani shago wanda yake tsakiya kafin ta warwatsu, ana zaton wutar lantarki ce ta haddasa ta.” Har ila yau, wani wanda abin ya shafa mai suna, Muhammadu Yusuf, wanda kuma yake da shagon sayar da zinare a kasuwar ya yi wa manema labarai karin bayani, inda ya ce ya yi “fiye da miliyan 60.”
Ba dai wannan ne karon farko na faruwar gobara ba a kasuwar, kimanin shekaru uku da suka wuce, sai da gobara ta tashi a wannan bangaren na kasuwar.