✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobara ta lakume shaguna a kasuwar waya ta Jagwal a Maiduguri

Wata gobara da ta tashi a kasuwar saye da sayarwar wayoyi da aka fi sani da “Kasuwar Jagol,” da ke garin Maiduguri babban birnin jihar…

Wata gobara da ta tashi a kasuwar saye da sayarwar wayoyi da aka fi sani da “Kasuwar Jagol,” da ke garin Maiduguri babban birnin jihar Borno ta lakume kayan miliyoyin Naira.

Gobarar ta fara ne da misalin karfe 8:00 na dare ranar Alhamis wanda ta dau awowi tana ci kafin jami’an kashe gobara su kashe wutar tare da hadin gwiwar jama’ar gari.

A cewar wasu rahotanni gobarar ta fara ne tun yammacin ranar Alhamis ta kai cikin daren Juma’a tana ci inda kuma ta yi wa shaguna 47 kurmus na kasuwar wayar ta Jagwal.