✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gobara ta lakume rayukan mutum 12 da dukiyar Naira miliyan 17 a Kano

Rayukan mutum 12 da dukiya ta naira miliyan 17.6 gobara ta lakume a fadin jihar Kano cikin watan Afrilun da ya gabata. Mai magana da…

Rayukan mutum 12 da dukiya ta naira miliyan 17.6 gobara ta lakume a fadin jihar Kano cikin watan Afrilun da ya gabata.

Mai magana da yawun Hukumar Kwana-Kwana ta jihar, Saminu Abdullahi ne ya bayyana wannan alkaluma ranar Talata cikin birnin Dabo.

Sai dai ya ce rayukan mutane da dama da dukiya ta kimanin naira miliyan 423 aka ceto cikin jihar a watan na jiya.

“Hukumar ta amsa kiran neman kawo agajin gaggawa guda 73 da kuma kiran bogi 14 daga mazauna a fadin jihar,” a cewarsa.

Abdullahi ya alakanta aukuwar mafi akasarin musibar da hatsarin mota, da sakaci wajen amfani da tukunyar iskar gas ta dafa abinci sannan kuma da rashin kula wajen amfani da kananan kayayyaki masu amfani da lantarki.

Ya shawarci mazauna jihar da su rika lura da yin kaffa-kaffa da ababen da suke amfani da su a zamantakewarsu domin gudun aukuwar gobara.

%d bloggers like this: