Wata gobara ta tashi a ofishin Hukumar Zabe ta kasa (INEC) da ke jihar Kano.
Gobarar wacce ta kama ta misalin karfe 9.00 na safiyar Talata, ta kone dukkanin sashen da ke tattara bayanan hukumar a wasu dakuna masu dauke da na’u’rorin komfuta.
- Direba da karen mota sun yi wa mai cutar HIV fyade
- Tsohon Mataimakin Shugaban Amurka, Walter Mondale ya mutu
Wani shaidar gani da ido ya bayyana wa wakilanmu cewa, sai da aka yi aikin hadin gwiwa tsakanin jami’an Hukumar kashe gobara na Tarayya da na Jihar gabanin kashe wutar.
“Bayan kimanin minti 20 da gobarar ta tashi ne jami’an kwana-kwana suka isa wurin, duk da cewa jinkirin zuwansu ya bayar da gudunmuwar asarar da aka yi amma dai sun samu nasarar kashe ta.”
Wasu daga cikin ma’aikatan hukumar da abin ya faru a gabansu, sun bayyana cewa gobarar ta auku ne a sakamakon wutar lantarki da aka kawo mai karfin tsiya wacce ta janyo fashewar wasu na’u’rorin sanyaya dakin da ke ginin.