✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobara ta kone shaguna a kusa da babban masallacin Zariya

Masu shagunan sun yi zargin hukumar kashe gobara ta ki kai musu dauki tsawon awa biyar

Wata gobara ta ƙone kaya na dubban Nairori a wasu shaguna da ke gefen masallacin Kofar Fadar Sarkin Zazzau da ke Zariya a Jihar Kaduna.

Masu shagunan sun yi zargin wutar da ta far ci tun misalin ƙarfe 2:00 na daren Juma’a, ta ɗauki kusan sa’o’i 5 tana ci ba tare da kai daukin gaggawa daga jami’an kashe gobara ba.

Da yake ƙarin haske kan faruwar lamarin, Kabir Ibrahim Wazirin Kasuwa ya yi zargin cewa wutar lantarkin da aka kawo misalin ƙarfe 2:09 na dare ce ake kyautata zaton ta sabbaba farawar lamarin.

Ya kuma ce duk ƙoƙarin da suka yi na kai rahoto ga jami’an kwana-kwana domin su kai musu ɗauki, ya ci tura saboda wasu matsalolin da suke fuskanta.

Sai dai ya yaba wa ƙoƙarin da jami’an tsaro da sauran al’umma suka yi na ba su kulawar da ya kamata lokacin faruwar lamarin.

Kabir Wazirin Kasuwa ya ce sun yi asarar kaya na maƙuden kudade wanda kuma suke buƙatar agajin gaggawa daga hukumomin da lamarin ya rataya kan su

Ya kuma buƙaci samar da ƙarin kulawa ga hukumomin da ke kula da kashe gobara don kai ɗaukin gaggawa lokacin da bukatar hakan ya taso.

Duk kokarin Jin ta bakin Kwamandan Kashe Gobara Mai kula da shiya ta daya Ummar Mohammad ya ci tura, kasancewar ba ya ofishinsa Kuma lambar wayarsa ba ta zuwa.

Amma wani jami’i a hukumar da ya nemi a sakaya sunansa ya ce suna fuskantar matsaloli na rashin isasshen man motar, inda ya ce wani lokacin ma har da rashin shi kansa ruwan da za su yi amfani da shi wajen kashe gobara idan aka kai musu rahoto irin haka.

Ya kara da cewa suna fuskantar wadannan matsalolin ne a daidai lokacin da aka fara shiga yanayin hunturu, wanda aka fi barazanar samun tashin gobara.