✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gobara ta kone shaguna 80 a Kasuwar Kurmi

Hukumar ta ce za ta gudanar da bincike kan musabbabin tashin gobarar.

Hukumar Kwana-Kwana ta Jihar Kano, ta ce gobara ta kone shaguna 80 a Kasuwar Kurmi da ke Karamar Hukumar Birni ta jihar

Sanarwar ta ranar Laraba mai dauke da sa hannun kakakin hukumar, Alhaji Saminu Abdullahi, ta ce gobarar ta tashi ne da misalin karfe 5:23 na safe.

Abdullahi, ya ce ma’aikatar ta samu kiran gaggawa daga wani Aliyu Alkasim cewa an samu tashin gobara a kasuwar.

Kakakin ya tabbatar da cewa gobarar ta kone shaguna 80, sai dai kuma an yi sa’a ba a samu asarar rai ba kuma babu wanda ya jikkata.

Ya kara da cewa ya zuwa yanzu ana ci gaba da gudanar da binciken musabbabin tashin gobarar.

Abdullahi ya shawarci mutane da su rika kashe na’uran wutar lantarki da kuma gujewa amfani da wuta musamman a harabar kasuwa.

Kamfanin Dillancin Labarai (NAN), ya ruwaito cewa Kasuwar Kurmi ta shahara wajen cinikin turare, kayan kawa da kayan fatu.