✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobara ta kone shaguna 7 a kasuwar Jos

Rahotanni na cewa, a jiya Laraba ne aka samu tashin gobara a kasuwar Gangare da ke karamar hukumar Jos ta Arewa jihar Filato. Gobarar dai…

Rahotanni na cewa, a jiya Laraba ne aka samu tashin gobara a kasuwar Gangare da ke karamar hukumar Jos ta Arewa jihar Filato.

Gobarar dai ta kai sa’o’i biyu tana ci kafin hukumar kashe gobara ta yi nasarar kashe wutar. Shugaban kungiyar ‘yan tireda na kasuwar Mahmood Sa’ad, ya bukaci gwamnatin jihar da gwamnatin tarayya da su tallafa wa wadanda suka yi asarar dukiyoyinsu.