Akalla shaguna hudu ne suka kone kurmus a kan titin zuwa filin jirgin saman Malam Aminu Kano a Karamar Hukumar Fagge a Jihar Kano.
Wannan na dauke ne cikin wata sanarwa da kakakin Hukumar Kashe Gobara ta jihar, Alhaji Saminu Abdullahi, ya fitar.
- ’Yan bindiga sun kashe likita yana cikin duba mara lafiya
- Kotu ta ba da belin matashin da ya sace kayan N4m
Ya ce lamarin ya faru ne a ranar Litinin.
“Mun samu kiran gaggawa da misalin karfe 9:06 na safe daga wani Hamish Ahmed, nan take muka tura jami’anmu zuwa wajen da misalin karfe 9:13 na safe don kashe wutar.
“Shagunan da suka kone ana harkokin kasuwancin sayar da kayan bandaki, kayan mota da kuma kayan asibiti,” in ji shi.
Ya ce har yanzu ba su gano musabbabin tashin gobarar ba amma hukumar na ci gaba da bincike don gano musabbabin.
Wannan dai na zuwa ne sa’o’i 24 bayan da hukumar ta fitar da rahoton cewa mutum 166 ne suka mutu a jihar sakamakon gobara daban-daban da ta tashi a shekarar 2022.