✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobara ta kone kamfanin sayar da kayan gado a Kano

Gobarar ta kone kamfanin baki daya tare da kama wasu gine-gine da ke kusa da shi.

Wata gobara ta kone kone wani kamfanin sayar da kayan gado na ‘Alibert Furniture’ da ke kan titin Murtala Mohammed a garin Kano.
Wani ganau mai suna Bello Ya’u, ya ce wutar ta tashi ne da sanyin safiyar Litinin, inda ta kone kamfanin kurmus tare da fara kama wasu gine-gine da ke jikin ginin kamfanin.
“Da safe wutar ta tashi lokacin muna kokarin neman abin da za mu ci. Kwatsam sai muka hangi mutane kowa na gudun ceton ransa.

“Mun je wurin don kai dauki amma muka kasa kashe gobarar saboda wutar ta kama sosai, har sai da jami’an hukumar kashe gobara suka zo kafin daga bisani su yi nasarar kashe ta.”

Aminiya ta yi kokarin gano abin da ya haddasa gobarar amma hakan ya ci tura, sai dai ana zargin wutar ta tashi ne daga matsalar wutar lantarki da aka samu, kuma an kasa kashe wutar ce sakamakon nau’in kayan da ke cikin kamfanin.

Mutum biyu daga cikin masu gadin kamfanin sun samu rauni kuma an garzaya da su zuwa asibiti, kamar yadda wani shaidar gani da ido ya bayyana mana.

Zuwa lokacin hada wannan rahoton, jami’an hukumar kashe gobara ta Kano sun kashe wutar.