Wata gobara ta yi sanadin konewar wani dan kasuwa, mai suna Malam Muntari da kuma salwantar dukiya mai yawa ta dubban Naira a yayin da ta ci dakunan kwanan baki da wasu shaguna a tsohuwar karar shanu ta Aduwawa da ke karamar Hukumar Ikpoba Okha a Jihar Edo a karshen makon da ya gabata.
Haka nan gobarar, wadda ta auku da misalin karfe shida na safiya, kamar yadda daya daga cikin ’yan kasuwa masu hada-hada a tsohuwar kasuwar, Malam Nafi’u A. Sani ya bayyana wa wakilinmu, ta yi barnar da har zuwa lokacin hada wannan rahoton ba a san adadinta ba.
Malam Nafi’u A. Sani ya ce, “Mun dawo daga sallar asuba da masalin karfe shida na safiya, kawai sai muka ga wuta ta tashi kuma hayaki ya turnuke daga dakin makwabcina Malam Muntari, kafin ka ce kwabo, wutar har ta tsallaka ta kama ci ga sauran dakuna da shagunan da ke kewaye da shi, gaba daya babu ta inda dan mutum zai sa kai. Amma, a cikin ikon Allah, jama’a da suka hada har da mata masu dafa abinci da suke a nan kasuwar sun taimaka sun kawo mana gudummawa ta gaske. Da wannan muka samu muka shawo kan wannan gobarar ba ta samu karfi yaduwa zuwa ta kama wasu sassan shaguna da suke a nan kasuwar ba. Mun gode wa Allah, domin in ba don taimakonSa ba da kuma samun yawan jama’a da suka kawo mana daukin gaggawa, Allah kadai Ya san iya asarar da ’yan kasuwanmu za su yi. Kuma, a gaskiya, duk da yawan asarar da gobarar ta janyo mana na salwantar kudade da shaguna da dakunan kwanan bakinmu, bai kai mana bakin ciki irin halin da abokinmu kuma dan uwanmu Malam Muntari yake a ciki a halin yanzu ba. Kasancewar yana kwance a asibti mai zaman kansa Medical Center a nan Aduwawa rai a hannun Allah sakamaon kunar wutar wannan gobarar da yake fama da ita, wannan muka fi damuwa da shi a halin yanzu.”
Wakilinmu ya je ofishin mai baiwa gwamna shawara a kan abin da ya shafi sha’anin harkokin ’yan Arewa mazauna jihar, Alhaji Sahabi Aliyu Umar (J.P.) domin samun karin bayani da kuma irin taimakon da gwamnatin jihar za ta iya yi wa ’yan kasuwar da bala’in ya shafa, amma abokan aikinsa sun ce ya fita ba ya ofis, wayarsa kuma a kulle take a yayin da ya nema.