Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kaduna ta tabbatar da mutuwar wani magidanci da iyalansa a sanadiyar wata gobara da ta auku a Zariya.
Mohammad Ummar, jami’in kashe gobara mai kula da shiyyar Zariya wanda ya bayyana hakan yayin ganawarsa da Aminiya ya ce gobarar ta auku ne ranar Alhamis da daddare.
Wakilinmu ya ziyarci gidan da gobarar ta auku a Layin Hajiya Mai Tuwo da ke Unguwar Low cost a Karamar Hukumar Zariya.
Ya zanta da makwabcin marigayin mai suna Safiyanu Aliyu, wadda ya ba da shaidar cewa gobarar ta yi sanadiyar mutuwar Muhammadu Sani da matarsa Raulatu Sani, sai dansu mai shekara takwas, Hashim Sani da kuma Fatima Sani ‘yar shekara daya da wata hudu da haihuwa.
Safiyanu ya ce “marigayi Muhammad Sani limami ne a masallacin gidan Barrister Muntaka da ke kan layin Buhari a unguwar nan ta mu.
“Muna kyautata zaton gobarar ta auku ne bayan an kawo wutar lantarki cikin dare,” a cewar makwabcin.
Wani dan sintiri mai suna Bello Haruna, ya kara shaida wa wakilinmu cewa suna cikin aiki rangadi a unguwa kamar yadda suka saba sai kawai suka hangi wuta, inda ya ce daga nan ne suka fara yekuwar jama’a su fito su kawo dauki.
A cewar Bello, yana zargin wutar lantarkin da aka kawo ce ta haddasa wannan gobara, kuma kafin a yi wata-wata ta lakume sashin da mai gidan da iyalinsa suke ciki.