Majalisar Dattawa ta dage zama daga yau har zuwa ranar Talata mai zuwa sakamakon wata ‘yar gobara da ake tunanin ta faro daga wani wayar wuta da ta samu matsala.
Cikin dan kankanin lokaci hayaki ya mamaye majalisar, wanda hakan ya sa ‘yan majalisar suka fito waje.
An fara ganin hayakin ne a lokacin da ‘yan majalisar na dattawa suke shigowa zauren majalisar domin gudanar da zamansu nay au.
Bayan hayakin ya sarara, sai majalisar ta zauna na kimanin minti biyar, sannan daga sai ta dage zaman har zuwa ranar Talata mai zuwa.