Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta ce mutane uku ’yan gida daya sun rasu bayan wata wuta ta tashi da sanyin safiyar Litinin kuma ta ritsa da wasu iyalai a unguwar Rijiyar Zaki dake cikin birnin Kano.
Kakakin hukumar, Alhaji Sa’idu Mohammed ne ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce ya faru ne misalin karfe 3:18 na dare kuma ta kone ilahirin gidan.
- Jarirai sabbin haihuwa 10 sun mutu a gobarar asibiti a Indiya
- Dangote ya tafka asarar Naira biliyan 342 a cikin sa’o’i 24
A cewarsa, “Mun sami kiran gaggawa daga wani mai suna Malam Salisu Muhammad da misalin karfe 3:18 wanda ya kawo korafin wutar na ci a wani gida dake da makwabtaka da shi da mutane uku a cikinsa.
“Da jin haka ba mu yi wata-wata ba muka tura jami’anmu masu ceto zuwa wurin da misalin karfe 3:22 na dare.
“An sami nasarar ceto su ciki halin rai-kwakwai, mutu-kwakwai daga bisani kuma aka garzaya da su Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad dake Kano amma likitan dake aiki ya tabbatar da sun riga sun rasu,” inji Kakakin hukumar.
Sa’idu ya ce wadanda suka rasun, Hauwa Musa mai kimanin shekaru 25, Mubarak Musa mai shekaru 13, sai kuma Salamatu Musa mai shekaru 20, dukkansu ’yan gida daya ne.
Sai dai ya ce har yanzu suna kan bincike domin gano musabbabin gobarar.