Akalla kantuna 91 ne suka kone kurmus bayan gobara ta tashi a kasuwar tufafi ta Kairo a Jiha Legas.
Gobarar ta tashi ne a ranar Alhamis da dare, amma ba a kai ga kashe ta ba sai a safiyar Juma’a.
- ’Yan fashi sun tare motar banki, sun daka wa kudin cikinta wawa
- Abaya: Yadda gasar kayan Sallah ke sanya mata a hadari
- ‘Maganarmu ta karshe da dana kafin masu garkuwa su kashe shi’
Darakta-Janar na Hukumar Agajin Gaggawat ta Jihar Legas (LASEMA), Olufemi Oke-Osanyintolu, ya ce “Da muka isa wurin mun samu wasu kantuna da ke a kulle suna ci da wuta.”
Ya ce ba a yi asarar rai ba, amma an gano wasu abubuwan fashewa a yayin kashe gobarar kasuwar da ke unguwar Oshodi, kuma ana bincike a kai.
Ofisoshin gudanawar kasuwar da shaguna daban-daban ne gobarar ta lakume baya ga dukiyoyin miliyoyin Naira da aka yi asara.
LASEMA da hukumar kwana-kwana da sauransu ne suka yi taron dangi kafin a samu a kashe wutar.