✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobara ta cinye kamfanin shinkafa ƙurmus a Kogi

Gobara ta laƙume wani kamfanin shinkafa ƙurmus a yankin Ega-Idah, Hedikwatar Ƙaramar Hukumar Idah a Jihar Kogi.

Gobara ta laƙume wani kamfanin casar shinkafa ƙurmus a yankin Ega-Idah, Hedikwatar Ƙaramar Hukumar Idah a Jihar Kogi.

Ganau sun ce da misalin ƙarfe 3 da dare kafin wayewar garin Alhamis ne gobarar ta tashi, bayan an ji ƙarar fashewar wani abu a wurin.

Sun bayyana cewa kamfanin da ke samar da shinkafar ga ’yan kasuwa a yankin ƙananan hukumomin Ibaji da Idah mallakin wasu ’yan kasuwa ne.

Wani shida ya ce wani mai gadi a kamfanin ya ba da rahoton jin sautin ƙyasta ashana kafin kafin ƙarar fashewar da aka ji a harabar kamfanin.

“Jim kaɗan bayan nan sai aka ji ƙarar fashewa da tashin wuta da ta laƙume ɗaukacin kamfanin.

“Rashin wutar lantarki a lokacin da abin ya faru ya sa masu gadin ba su iya gane wanda ake zargi ba.

“Lokacin bukukuwan Kirsimeti ne harkarmu ta tafiya, amma kuna sai wannan abin takaici ya faru,” in ji wani ɗan kasuwa mai harkar shinkafa a yankin.

Ya ce ƙonewar kamfanin wanda kudinsa ya kai Naira miliyan 200 zai shafi yanayin tattalin arzikin yankin musamman a wannan lokaci na bukukuwa da ake neman shinkafa sosai.

Har yanzu dai ba a gano ainihin musabbabin gobarar ba, amma mazauna yankin sun bukaci mahukunta su gudanar da bincike domin hana faruwar hakan a nan gaba.

Ƙoƙarin wakilinmu na magana da kakakin ’yan sandan Jihar Kogi SP Williams Aya bai yi nasara ba. Ya kira wayar jami’in ya kuma rura nasa rubutaccen sako, amma duk babu amsa.