✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gobara ta cinye Babbar Kasuwar Mokwa

Wutar da ta fara ci da asubar fari ta kusa cinye ’yan kasuwar da ke kwana a cikin shagunan kasuwar

Dukiya ta makudan kudi ta salwanta a sakamakon wata gagarumar gobara da ta tashi a Babbar Kasuwar Mokwa da ke Jihar Neja.

Gobarar da ta tashi a cikin da asubar fari ta kusa cinye wasu ’yan kasuwar da ke kwana a cikin kantunansu, amma sun sha da kyar da raunuka a jikinsu, an kai su Babban Asibitin Mokwa inda suke samun kulawa.

Basaraken garin, Ndalile-Mokwa, Alhaji Mohammed Shaba, ya ce wutar ta cinye fiye da rabin kasuwar, “Da misalin karfe 4 na asuba, aka kira ni shi ne na kira hukumar kashe gobara. Sun yi ta kokarin kashe wutar, amma saboda rashin motoci, yanzu haka wutar tana nan tana ci.”

Ya ce bata-gari sun yi amfani da damar wajen sace kayan, amma an yi nasarar kama wasu daga cikinsu.

%d bloggers like this: