✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobara ta ci shaguna a kasuwar Kurmi

Gobara ta ci wasu shaguna biyu a kasuwar Kurmi da ke birnin Kano a ranar Talatar da ta gabata.Kamar yadda wasu rahotanni daga birnin suka…

Gobara ta ci wasu shaguna biyu a kasuwar Kurmi da ke birnin Kano a ranar Talatar da ta gabata.
Kamar yadda wasu rahotanni daga birnin suka bayyana, gobara ta tashi
ne da misalin karfe takwas na daren ranar Talatar da ta gabata.
Wani ganau wanda yake da shago a kasuwar, Auwalu Skido Mai riguna, ya shaida wa BBC cewa shaguna biyu ne na kayan doki suka kone.
Mutumin ya ce bayan da suka ga wutar na ci a shagunan saboda gudun kada ta kama sauran shaguna, sai suka kira jami’an kashe gobara, kuma ba da jimawa ba suka zo suka kashe wutar.
Ya kuma kara da cewa akalla kayan da suka kone a shagunan sun kai na naira miliyan uku. Ba a dai samu asarar rai ko daya a gobarar ba. Wannan dai ba shi ne karon farko da gobara ta tashi a kasuwar ba, don a baya an sha samun faruwar hakan.