✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobara ta ci shaguna a Kasuwar Gandun Albasa

A safiyar shekaranjiya Laraba ne wata gobara ta tashi a Kasuwar Kujeru da Gadaje da ke Gandun Albasa a yankin karamar Hukumar Birnin  Kano, inda…

A safiyar shekaranjiya Laraba ne wata gobara ta tashi a Kasuwar Kujeru da Gadaje da ke Gandun Albasa a yankin karamar Hukumar Birnin  Kano, inda shaguna fiye da 15 suka kone kurmus.
Gobarar wacce ake zaton barayi ne suka sa ta, ta lakume kayayyaki na miliyoyin Naira. Shugaban Kasuwar Mista Steben Kanu Elemu ya bayyana cewa yana gida da misalin karfe biyar na Asuba aka buga masa waya cewa ga gobarar ta tashi a kasuwarsu.
 “Bayan an sanar da ni a take na yi gaggawar zuwa wurin inda na iske a lokacin ma wutar ta cinye kimanin shaguna 15. Da muka kiyasta kayayyakin da ta ci wanda ya hada da katakai da wasu gadaje da kujeru sun fi Naira miliyan 15,” inji shi.
Da yake bayanin dalilinn tashin gobarar Shugaban ya bayyana cewa “duk da yake ba mu san gaskiyar lamarin ba, amma daga labarin da aka ba ni an ce a cikin dare wasu wanda ake zaton barayi ne sun shigo kasuwar da niyyar yin sata, to sai ’yan sintiri da ke unguwar suka kore su. To sai daga baya kuma sai suka dawo suka sa wutar.”
Wani daga cikin wadanda suka yi asara a gobarar mai suna, Muhmamdu Madugu ya bayyana cewa ya yi asara fiye da Naira miliyan biyar, don haka ya yi kira ga gwamanti da ta taimaka musu don su sami su farfado da harkar kasuwancinsu.
Mista Steben ya yi kira ga gwamnati da ta kawo musu dauki “muna rokon gwamnati da ta taimaka mana kasancewar wannan ba shi ne karo na farko da gobarar ta tashi a wannan kasuwar ba, domin a watan Nuwambar bara ma gobarar ta tashi a dai wannan wurin, inda ta ci dukiya ta miliyoyin Naira. Don Allah gwamnati ta taimaka asarar da muka yi ta yi yawa,” inji shi.