✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gobara ta ci ofishin ’yan sanda a Kano

Gobara ta tashi a Babban Ofishin ’yan sanda da ke unguwar Dakata a Jihar Kano.

Gobara ta tashi a Babban Ofishin ’yan sanda da ke unguwar Dakata a Karamar Hukumar Nassarawa a Jihar Kano.

Kwamishinan yan sandan jihar, Usaini Gumel, ya ce gobarar ta safiyar Litinin, “ta kone wani bangare gaba daya a babban ofishin ’yan sandan da ta tashi.

“Amma duk haka, babu abin da ya sami makaman da ke ofishin.”

Kwamishinan ’yan sandan ya ce tashin gobarar ke da wuya, jami’an hukumar kashe gobara ta jihar suka zo suka kashe ta, kuma ana bincike don gano musabbabin tashinta.

“An killace wurin domin hana masu kallo da miyagu shiga, kuma DPO na yankin yana kan tantance wasu takardun da abin ya shafa,” inji shi.