✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobara ta ƙone shaguna da kayan miliyoyi a kasuwar Nasarawa

'Yan kasuwar sun koka kan rashin kyakkyawan tsarin kashe gobara a kasuwanni jihar.

Gobara ta tashi a kasuwar Masaka da ke Ƙaramar Hukumar Karu a Jihar Nasarawa a daren ranar Juma’a, inda ta ƙone shaguna da kayan miliyoyin Naira.

Shaidu sun ce wutar ta tashi ne misalin ƙarfe 11:45 na dare, inda ta bazu zuwa shagunan da ke sayar da kayan masarufi da na lantarki.

Wani ɗan kasuwa, Musa Hudu, wanda shagonsa ya ƙone ƙurmus, ya ce wutar ta lalata musu dukiya.

“Mun dogaro da shagunanmu don ciyar da iyalanmu, amma yanzu komai ya ƙone,” in ji shi, inda roƙi gwamnati da jama’a su taimaka musu.

Wani ɗan kasuwa, John Samuel, ya zargi jinkirin isowar masu kashe gobara, wanda ya ce sun iso bayan an yi asara mai yawa.

Ya nemi gwamnati ta samar da kyakkyawan tsari. kashe gobara a kasuwannin jihar.

Hukumar kashe gobara ta Jihar Nasarawa, ta tabbatar da faruwar lamarin.

Amma ta ce sun samu jinkiri saboda lalacewar motarsu.

Har yanzu ana bincike don tantance yawan shagunan da suka ƙone.

Wannan shi ne karo na biyu da irin wannan gobarar ta faru a jihar a kwanan nan, bayan gobarar da ta tashi a Kasuwar Lafiya, inda shaguna 30 suka ƙone.

Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa, ta riga ta amince da ƙudirin kafa Hukumar Kashe Gobara don samar da kayan aiki da inganta tsaron wuta a jihar.