Kayayyakin miliyoyin Naira sun salwanta sakamakon tashin gobara a shaguna kasuwar garin Jattu ta Uzairue, a Ƙaramar hukumar Etsako ta Yamma da ke Jihar Edo.
An samu rahoton cewa gobarar ta tashi ne da safiyar Laraba daga shagunan da suke daura da kasuwar Jattu kan hanyar Auchi zuwa Agenebode.
- Ya cinna wa matarsa wuta, ya kai kansa ofishin ’yan sanda
- Turkiyya ta dawo da sufurin jiragen sama zuwa Syria bayan shekara 13
An ruwaito cewa gobarar ta tashi ne daga wata tukunyar gas ɗin girki a ɗaya daga cikin shagunan.
A wani bidiyo da ke nuna yadda gobarar ta tashi, ‘yan kasuwa da masu jajantawa sun yi ƙoƙarin kashe wutar sakamakon babu jami’an hukumar kashe gobara a yankin, amma hakan bai yi nasara ba.
Aminiya ta samu rahoton cewa, ba a samu asarar rai ba a gobarar amma kayayyakin da suka kai na ɗaruruwan miliyoyin Naira aka yi asarar su a kasuwar.
A yanzu dai gwamnan Jihar Edo, Monday Okpebolo ya jajanta wa ‘yan kasuwar da suka yi asarar kayayyakinsu a tashin gobarar.
Ya koka da cewa, wannan mummunan lamari ya janyo asarar dukiya da rayuwa mai yawa, ya kuma bada tabbacin ’yan kasuwar da abin ya shafa gwamnatin jihar ta himmatu wajen bayar da dukkan taimakon da ya kamata.
“Gwamnati tana aiki kafaɗa da kafaɗa da hukumomin da abin ya shafa da suka haɗa da hukumar kashe gobara, hukumar bada agajin gaggawa ta jihar da kuma ƙaramar hukumar domin tantance asarar da aka yi tare da bayar da agajin gaggawa,” in ji shi.