✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobara: Mutum 100 sun rasu, an ceto 417 a Kano a 2023

Kakakin hukumar ya ce sun samu kiran agaji guda 659 a 2023.

Mutane akalla 417 ne suka tsallake rijiya da baya daga gobarar da aka samu a Jihar Kano  shekarar 2023.

Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, ta sanar cewa wasu mutum 100 sun rasa rayukansu, yayin da aka yi asarar kadarorin sama da Naira miliyan 45 a fadin jihar a shekarar.

Kakakin hukumar, Saminu Abdullahi ne, ya shaida wa da kamfanin dillacin labaran Najeriya (NAN), cewa sun samu kiran neman agaji 659 a shekarar.

A cewarsa, jami’ana sun kuma yin asarar da  ce daukiyar biliyan N1.2 daga gobara a wurare daban-daban a shekarar.

Abdullahi ya ce sun amsa kiran agaji na gaskiya 299 da kuma na karya 95 daga mazauna jihar da kuma kiran agaji 184 a kan hatsarin titi.

Kakakin ya danganta tashin gobarar da rashin kula da gas din girki, amfani da na’urorin lantarki da adana man fetur a gidaje da sauransu.

Ya shawarci al’ummar jihar da su yi taka-tsan-tsan yayin da suke sarrafa abubuwan da ka iya haifar da gobara.

“Masu jin dumi musamman a lokacin sanyi a kasuwa ko bakin titi, ya kamata su kashe wutar da isasshen ruwa don guje wa yanayin da ba a shirya masa ba.

“Ya kamata iyaye su kasance masu sanya ido kan ’ya’yansu, musamman wadanda ke zuwa rafi wanka don guje wa nutsewa ko wani abu daban,” in ji shi.