✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobara a wajen ajiye man fetur ta kashe mutum 35 a Kwatano

Garin da gobarar ta auku ya yi kaurin suna wajen fasakwaurin mai daga Najeriya

Akalla mutum 35 ne suka mutu a Jamhuriyyar Benin bayan wani wajen ajiye man fetur ya kama da wuta sannan ya yi bindiga.

Gobarar dai ta tashi ne ranar Asabar a wani wajen ajiye kayayyaki da ake amfani da shi domin tara man da aka yi fasakwaurin shi a garin Seme-Podji da ke kusa da kan iyakar kasar da Najeriya.

Garin dai ya yi kaurin suna wajen tara man da aka yi fasakwaurin na shi inda suke tara shi ta hanyar amfani da babura da motoci.

Wani jami’in gwamnati a yankin, Abdoubaki Adam Bongle, ya ce, “Gobarar ta kone dakin, kuma binciken farko-farko ya nuna akalla mutum 35 sun mutu, ciki har da wani karamin yaro.

“A cewar wasu ganau da aka zanta da su, watakila, wutar ta tashi ne lokacin da ake kokarin sauke man.”

Ya kuma ce sama da mutum 12 sun samu munanan raunuka kuma suna karbar kulawa daga likitoci a asibiti.

Wani bidiyo da ya rika yawo a kafafen sadarwa ya nuna yadda hayaki ya turnuke sararin samaniyar wani waje da aka yi ittifakin kasuwa ce, yayin da mutane ke tsaye daga gefe suna kallo.

Ministan Harkokin Cikin Gidan Kasar, Alassane Seidou ya ce man da ake fasakwaurinsa shi ne musabbabin gobarar.

Fasakwaurin mai dai sana’a ce da ta yi kaurin suna a Benin da ma sauran kasashe makwabtan Najeriya.