✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Giroud ya tsawaita kwantiraginsa a Chelsea

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta zabi tsawaita kwantiragin dan wasan Faransa, Olivier Giroud, da shekara guda. Wata majiya ta shaida wa kamfanin dillancin labarai…

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta zabi tsawaita kwantiragin dan wasan Faransa, Olivier Giroud, da shekara guda.

Wata majiya ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa an tsawaita kwantiragin ne har zuwa watan Yunin 2021.

A shekarar 2018 ne dai Giroud, mai shekara 33 da haihuwa, ya koma Chelsea daga abokiyar adawarta ta birnin London, Arsenal.

Dan wasan ya ci wa Faransa kwallo 39 a wasa 97, lamarin da ya sa ya zama mutum na uku da ya fi ci wa kasar tasa kwallo bayan Michel Platini (mai 41) da Thierry Henry (mai 51).

Dan wasan na sa ran taka leda yayin Gasar Kwallon Kafa ta Nahiyar Turai badi.

%d bloggers like this: