✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Girgizar kasar Turkiyya: Yawan matattu ya haura 1,900

Wadanda suka rasu a Turkiyya sun kai 1,121 da wasu 810 a Syria baya ga wasu 783 sun jikkata.

Adadin mutanen da suka rasu a girgizar kasar da aka samu a kasar Turkiyya ya haura mutum 1,900 a kasar da kuma makwabciyarta, Syria.

Turkiyya sun ce wadanda suka rasu a kasar sun karu zuwa 1,121, a yayin da wasu 783 suka samu raunuka.

Hukumomin Syriya sun ce yawan mutanen da suka rasu a kasar sakamakon girgizar kasar ta safiyar Litinin ya karu zuwa sama da 810, wanda ya sa adadin haura mutum 1,900.

A safiyar Litinin ne aka samu girgizar kasar mai karfin maki 7.8, wadda aka ji ruguginta har a yankin Gaza da ke gaba da Syria aka ji.

Hukumomin ceto na ta kokarin ceto mutane da suka makale a cikin baraguzan gini da sauran wadanda lamarin ya shafa domin sama musu kayayyakin jin kai.