Kawo yanzu, rahotanni sun ce yawan wadanda suka mutu a girgizar kasar da ta auku a kasashen Turkiyya da Siriya ranar Litinin sun haura 2,300.
Girgizar kasar wanda karfinta ya kai 7.8, ta lalata galibin biranen Turkiyya a yankunan da a nan galibin ’yan gudun hijira daga Siriya suke da zama.
- Girgizar kasa: Kasashen na rige-rigen tallafa wa Turkiyya da Siriya
- Karancin kudi da wahalar fetur sun haifar da zanga-zanga a Ibadan
Shugaban Cibiyar Kula da Girgizar Kasa na Kasar Siriya, Raed Ahmed, ya ce “Wannan ita girgizar kasa mafi karfin da cibiyar ta taba gani a tarihinta.”
An ga masu aikin ceto na ta kokarin bincike domin gano mutane da kasa ta rufta da su, walau a raye ko a mace.
Akalla mutum 810 aka ce sun mutu Siriya, sannan 1,498 a Turkiyya kamar yadda jami’au suka bayyana.
Kafin wannan lokaci, girgizar kasa mafi muni da Turkiyya ta gani ita ce wadda ta auku a 1939 inda mutum 33,000 suka mutu.