✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Girgizar Kasa: Turkiyya na neman tallafi daga Najeriya

Kasar ta bukaci Najeriya ta tallafa mata da kayan agajin jin kai don taimakon wadanda abun ya shafa.

Gwamnatin Turkiyya ta nemi tallafin kayan jin kai daga Najeriya ga wadanda girgizar kasa ta shafa a kasar.

Ofishin Jakadancin Turkiyya a Najeriya ya bayyana hakan ne a wata sanarwa ranar Juma’a a Abuja.

Ofishin ya ce za a aike da kayayyakin ga wadanda abin ya shafa ne ta hannun Kamfanin Jiragen Sama na Turkiyya.

Sanarwar ta ce “Ga masu son bayar da gudummawa ta musamman ga wadanda iftila’in girgizar kasa ya shafa a Turkiyya.

“Za a yaba da gudummawar abubuwan da aka fi bukata kamar su: Tufafi: kayan sanyi na manya da na yara, rigunan ruwa, takalma, wanduna, safunan hannu, mayafin wuya, da manyan riguna.

“Sauran abubuwan su ne tantuna, katifu, barguna, shimfidar barci, jakunkuna da janareta.

“Abincin gwangwani, abincin jarirai, madara, kunzugun yara da na manya.

“Da fatan za a sanya kayayyakin a cikin jakunkuna masu haske kuma a bayyana abubuwan da ke cikin kowace jaka.

“Za a aika da tallafin Turkiyya ta hannun Kamfanin Jirgin Saman Turkiyya.

“Adireshin da za a aike da tallafin a Abuja shi ne;  Lamba 46 Aminu Kano Crescent, Wuse 2 Abuja.

A Legas kuma, ARMADA lnternational Limited, titin Solomon Agbonton (titin Aerodrome)”.

Girgizar kasar dai ta afku ne a ranar 6 ga watan Fabrairu, a wasu garuruwan Kudu maso Gabashin Turkiyya da Syria, inda ta kashe mutum sama da 22,000 tare da jikkata wasu dubbai sannan ta raba wasu da muhallansu.

Shugaba Recep Erdogan ya ayyana dokar ta baci a kasar Turkiyya tare da neman agajin jin kai na kasa da kasa.