Biyo bayan girigizar kasar da ta hallaka sama da mutum 1,000 a Afghanistan, gwamnatin Taliban da ke kasar ta bukaci kasashen duniya da su taimaka su bude asusun ajiyarta da suka toshe a kasashensu.
Girgizar kasar dai wacce tana daya daga cikin mafiya muni a tarihin kasar ta raba dubban mutane da muhallansu.
- Mutum 17 sun mutu a wajen sharholiya a Afirka ta Kudu
- Jirgin farko dauke da maniyyatan Gombe 508 ya tashi zuwa Saudiyya
Tun da Taliban ta kwace mulkin Afghanistan a watan Agustan bara dai take fama da rashin kudaden ayyukan raya kasa saboda rufe asusunta da ke kasashen ketare.
Tun lokacin dai kasar ke fama da mawuyacin matsin tattalin arziki sakamakon rike biliyoyin Dalolinta da kuma jerin takunkumai iri-iri da kasashe suka yi, lamarin da ya jefa masu mulkin kasar cikin halin ni’ya-su.
Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen kasar, Abdul Qahar Balkhi, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa, “Masarautar Musulunci ta Afghanistan na kira ga kasashen duniya da su ba ta abin da yake halal din ta, ta hanyar cire mata takunkumai da kuma sake bude kadarorinta da aka kulle.”
Ya ce kamata ya yi duniya ta yi la’akari da irin tsananin bukatar da kasarsu ke ciki wajen neman ceto rayuwar mutanenta sama da komai.
Girgizar kasar dai wacce ta fada wa kasar ranar Larabar da ta gabata, ta lalata gidaje sama da 10,000, sannan ta jikkata sama da mutum 2,000.
Lamarin dai ya sake jefa bangaren lafiyar kasar da dama yake fama da kalubale cikin mawuyacin hali.
Taliban dai ta yi alkawarin cewa za ta bar kayan agajin da ake turawa kasar su isa hannun mutanen da suka fi bukatar shi.