✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Girgizar kasa ta kashe mutum 56 a Indonesia

Girgizar kasa mai karfin maki 5.6 a ma’auninta ta afku ne a tsibirin Java na kasar Indonesia.

Akalla mutane 56 ne suka mutu sakamakon wata girgizar kasa da ta afku a tsibirin Java na Indonesia a ranar Litinin.

Adam, kakakin karamar hukumar Cianjur a yammacin Java, wanda kamar yawancin ‘yan Indonesiya ke da suna daya, ya shaida wa AFP cewa wannan adadi ne na wucin gadi ne saboda ba’a kai ga tantance adadin ba, inda gidaje da dama suka lalace.

Girgizar kasa mai karfin maki 5.6 a ma’auninta ta afku ne a tsibirin Java na kasar Indonesia a ranar Litinin, inda ta kashe mutane da dama tare da lalata gine-gine da kuma haddasa zabtarewar kasa.

Babban jami’in da ke yankin yammacin Java da girgizar kasar ta fi kamari, ya ce an kidaya wadanda suka mutu a asibiti daya kadai, ba tare da bayar da takamaiman adadi ba, yayin da wasu mutane da dama suka makale a wasu kauyuka da har yanzu ba a kai ga kwashe su ba.

Ya ce ‘yan uwan ​​wadanda lamarin ya rutsa da su sun taru a asibitin Sayang da ke garin, ya kuma yi gargadin cewa adadin wadanda suka mutu na iya karuwa saboda har yanzu mazauna kauyukan da ke wajen garin na cikin makale.