Wata mummunar girgizar kasa a tsibirin Java na kasar Indonesia ta rusa gidaje da dama, ta kuma halaka mutum 17, yayin da ake fargabar adadin zai iya karuwa.
Hukumar Binciken Yanayin Kasa ta Amurka ta ce girman girgizar ta ranar Litinin ta kai kusan maki 5.6 kuma ta faru ne a yankin Cianjur mai nisan kilomita 10 a yammacin Java.
- Matsalar wutar Lantarki: Ganduje zai yi rusau a Kano
- Mutum 9 sun rasu bayan motarsu ta fada cikin Dam a Kano
Lamarin dai ya sa mazauna Jakarta, babban birnin kasar sun rika guduwa tituna don neman tsira da rayukansu.
Girgizar dai ta halaka akalla mutum 17 sannan ta jikkata wasu da dama, inji Hukumar Kiyaye Bala’o’i ta Kasar. Gine-gine da dama ne, ciki har da wata makarantar kwana ta Islamiyya da asibiti da sauran gine-ginen gwamnati ne suka lalace.
Herman Suherman, wani jami’in gwamnati a Cianjur, ya shaida wa gidan talabijin na Metro cewa akalla mutum 20 ne suka rasu, wasu 300 kuma suka ji rauni. Sai dai ya ce akwai fargabar adadin zai iya karuwa.
A cewar Adam, Kakakin Karamar Hukuma a garin na Cianjur, gwamman mutane ne suka rasu a garin mai nisan kimanin kilomita 75 a Kudu maso Gabashin Jakarta, kamar yadda ya sahida wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa (AFP).
“Akwai gwamman mutane da suka rasu. Darururwa, ko ma dubbai sun lalace. Yanzu haka, mutum 44 sun rasu,” inji Adam, wanda kamar ’yan kasar da dama ke amfani da suna daya.
Wasu hotunan bidiyo na gidan talabijin din na Metro sun nuna yadda wasu gine-gine da dama a yankin na Cianjur suka rushe baki daya, yayin da mutane ke cikin matsananciyar damuwa.