✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Girgizar kasa: Kasashe na rige-rigen tallafa wa Turkiyya da Siriya

Adadin wadanda suka mutu a girgizar kasar ya kai 1,900

Rahotanni sun ce adadin mutanen da suka mutu sakamakon iftila’in girgizar kasar da Turkiyya da Siriya suka fuskanta ya kai 2,300.

Ganin halin da kasashen biyu suka tsinci kansu ya sa kasashe da dama suka kuduri aniyar tallafa musu gwargwadon hali.

Aminiya ta tattaro muku jerin wadannan kasashe da gudunmawar da kowacce ta shirya bayarwa:

China

Kasar China ta ce za ta ba da gudunmawar jinkai ga kasahsen biyu. Ta bayyana hakan ne ta hannun hukumar ba da agaji a ketare, sai dai ta bayyana takammen gudunmawar da ta shirya bayarwa ba.

Kasar ta nuna alhini da mika ta’aziyya ga gwamanatocin kashen da lamarin ya shafa dangane da rashin da ya same su.

Kungiyar Tarayyar Turai

Hukumar Tarayyar Turai ta ce ta tura tawagar masu aikin ceto da aka tattaro daga kasahen Turai takwas zuwa Turkiyya. Bulgaria da Croatia da Tarayyar Czech  da Faransa da Girka da sauransu, na daga kasashen da aka tattaro jami’an tawagar aikin ceton.

Jamus

Jamus ma ta bi sahu, inda ta shirya ba da agaji ta hanyar samar da matsuguni ga wadanda lamarin ya shafa, kamar dai yadda Ministar Cikin Gidan Kasar, Nancy Faeser, ta bayyana.

Girka

Firan Ministan Girka, Kyriakos Mitsotakis, ya jajanta wa kasashen biyu kan abin da ya faru da su. Ya ce kasarsa na shirin ganin yadda za ta agaza wa Turkiyya nan ba da jimawa ba.

Indiya

Gwamnatin Indiya ta ce tuni ta hada kan tawagar kwararrun masu bincike su 100 da za ta tura Turkiyya a matsayin tata gudunmawa. Ta ce ta riga ta tura tawagar likitoci da kuma kayayyakin masarufi zuwa kasar.

Iran

Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Kasar Iran, Nasser Kanaani, ya ce su ma a shirye suke su tallafa wa kasashen biyu game da iftila’in da ya same su.

Ya ce taimako abu ne wanda rayuwa ke bukata kuma Musulunci ya tabbatar da shi.

Italiya

Ita kuwa kasar Italiya cewa ta yi ta shirya tsab don bada agajin gaggawa na kula da lafiya da kayan masarufi.

Qatar

Mai Martaba Sarkin Qatar, Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani, ya mika ta’aziyyarsa ga Shugaban Turkiyya,  Recep Tayyip Erdogan, ta waya. Tare da cewa za su ba da gudunmawarsu domin rage wa kasar radadin bala’in da ya afka mata.

Sauran Kasashe

Sauran kasashen sun hada da Isra’ila da NATO da Poland da Spaniya da Rasha da Ukraine da Ingila  da Amurka da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) da sauransu.