✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gina kasuwannin magunguna don tsabtace sana’ar

Yaki da miyagun magunguna da `yan jabu na daga cikin yakin da wannan gwamnatin ta jam`iyyar APC ta kara daura damara akai, bisa ga irin…

Yaki da miyagun magunguna da `yan jabu na daga cikin yakin da wannan gwamnatin ta jam`iyyar APC ta kara daura damara akai, bisa ga irin yadda kasar nan ta yi kaurin suna a kan sha da fataucin miyagun kwayoyi a idanun duniya. Don cimma wannan kuduri ne, ya sanya gwamnatin tarayyar ta bayar da wa`adin 31 ga watan Yulin da ya gabata, ta zama ranar karshe ga dukkan masu hada-hadar da sayar da magunguna da suke cikin wasu kasuwannin manyan biranen kasar nan da ake hada-hadar magunguna da su tattara yanasu-yanasu su bar cikin kasuwannin.

Kafin cikar wa`adin kuma sai ga Ma`aikatar Kiwon lafiya ta tarayya ta fitar da wata sanarwa, inda ta kara wa`adin da kimanin shekara daya da rabi, wato zuwa 31 ga watan Disambar 2018. Mai yiwuwa kara wa`adin ba ya rasa nasaba da irin matsin lambar da masu sana`ar sayar da magungunan a cikin kasuwannin suka rinka yi wa gwamnatin a kan sai ta kara wa`adin da kuma irin yadda ita kanta gwamnatin ba ta shirya komai ba wajen ganin tabbatuwar fitar da masu sayar da magungunan daga cikin kasuwannin, don kuwa har karewar wancan wa`adi, gwamnatin tarayyar ba ta gina ko da kasuwa daya ba a cikin manyan garuruwan Aba da Legas da Kano da Anacha, garuruwan da gwamnatin take zargin ana cin kasuwar magungunan kasar nan da kaidi, inda kuma nan za ta samar da kasuwannin magungunan.

A ranar 12-08-2017, an ji Ministan Lafiya Farfesa Isaac Adewole yana sake jaddada wancan wa`adin 31-12-2018,na gwamnatin tarayya a kan hana sayar da magunguna a cikin dukkan kasuwannin kasar nan da ta alkawarta tun farko. Ministan ya fadi hakan ne a Oba kusa da garin Anacha na Jihar Anambara lokacin da yake duba filin da za a gina katafariyar kasuwar hada-hadar magungunan, daga cikin wadancan garuruwa hudu da na ambata tun farko. Wa`adin da ministan ya ce ba sauran daga kafa a kansa daga ranar 01-01-2019.

“Daga waccan rana, muddin ba ka cikin wannan kasuwa ta magani, to kuwa ba inda kake a wannan sana`a.” Daga karshe ministan ya yaba wa Gwamnatin Jihar Anambara bisa ga irin hadin kai da goyon bayan da take ba aikin gina kasuwar magungunan ta Anacha, inda kuma ya nemi shugabannin kasuwar magungunan na Anacha da lallai su hada kansu, su kuma warware takaddamar da ke tsakaninsu.

Ministan ya ci gaba da cewa “Watakila mutane suna tsammanin gwamnati da wasa take, gwamnati ba ta wasa. Ba mu son magunguna `yan jabu da wadanda wa`adinsu ya kare aka canja masu takarda ko mazubi da sunan wa`adinsu bai kare ba, don a nuna suna da inganci. Muna son magunguna masu inganci kawai, shi ya sa muke son samar da kasuwar hada-hadar magunguna wuri guda, ta yadda za mu iya tantance sahihanci da wa`adin ko akasin hakan a kan irin magungunan da suka shiga ko suka fita,” In ji Farfesa Adewole.

Hada-hadar sayar da magunguna `yan jabu ko wadanda wa`adinsu ya kare ko masu sa maye barkatai a kasar nan ba wani sabo ko babban labari ba ne. Kasancewar Hukumomin kasar nan, tun daga sama har kasa ba sa kulawa wajen tabbatar da cewa kwararru a fannin kiwon lafiya irinsu likitoci ko masu ilmin harhada magunguna kadai suke rubuta ko bayar da maganin ga marasa lafiya. Ka iya cewa ta ci barkatai ake ta yadda kowa Likita ne ko mai iya ba da magani ne, wasu ma jin labarin ingancin magani kawai za su yi ga abokai ko makwabta, sai kawai su tafi dakunan sayar da magunguna, su saya. 

Samuwar hakan tabbatas ba su rasa nasaba da irin yadda harkokin kiwon lafiya suka yi mummunar tabarbarewa a kasar nan tun daga sama har kasa, ta yadda walau gwamnatin tarayya ko gwamnatocin jihohi, balle kuma na Majalisun kananan Hukumomi da za su bugi gaba su ce komai ya ji a asibitocinsu, walau a kan kayayyakin aiki ko ingantattu da wadatattun magunguna, balle kayayyakin aiki ko su kansu ma`aikatan kiwon lafiya.Wannan ta sa jama`ar kasa suke ganin zuwa asibitocin hukumomi tamfar bata lokaci ne. Hakan ta sa shan magunguna barkatai da kan sa wasu su zama `yan kwaya, don kuwa masana kiwon lafiya kan ce shan magani ba tare da umurnin Likita ba tamfar shan miyagun kwayoyi ne.

Jihar Kano ta yi matukar kaurin suna a kan shan miyagun kwayoyi a `yan shekarun nan, ta yadda  Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi, wato NDLEA a rahotonta na shekara-shekara, takan bayyana jihar a zaman jihar da ke kan gaba a kan sauran jihohin kasar nan a kan shan miyagun kwayoyi. Rahoton hukumar yana kiyasi ne a kan yadda ake shan miyagun kwayoyi na al`ada irin su bula da fetur da kashin kadangare da ma shakar shadda da makamantan abubuwan da suke sa maye, baya ga kwayoyi irin na Nasara da a yau wasu suka mayar da su miyagun kwayoyi, na sha a yi maye.

Kasuwar Muhammadu Abubakar Rimi da aka fi sa ni da Kasuwar Sabon gari, ita ce kasuwar da Mahukunta suke zargin nan ake hada-hadar wadancan miyagun kwayoyi, shi ya sanya Kanon ta zama daya daga cikin manyan garuruwa hudun da za a gina kasuwar magungunan yanzu. 

Wannan kaurin suna da Kanon ta yi, ba ko shakka, shi ya sa a shekarar 2012, tsohon Gwamna Kwankwaso ya yi kokarin kutsawa cikin Kasuwar ta Sabon gari da tsakar dare da aniyar ya rushe dukkan rumfunan masu sayar da magunguna, yunkurin da bai yi nasara ba, bisa ga irin yadda masu sayar da magungunan a daren suka yi barazanar muddin tsohon gwamnan ya cikasa alkawarinsa, to kuwa a daren za su kona kasuwar kowa ya rasa.

Daga bisani tsohon gwamnan ya ba masu sayar da magugunan  wa`adin karshen shekarar 2012, da su fice daga kasuwar, unmurnin da rashin gamsuwa da shi ya sanya `yan kasuwar maganin suka garzaya gaban wata Babbar kotun tarayya da ke Kano, inda suka kalubalanci umurnin, shari`ar da har ya zuwa wannan lokaci ba a yanke hukunci ba.

Su wadancan Kasuwanni da gwamnati tarayyar za ta samar za su zama karkashin kulawar `yan kungiyar masu ilmin hada magunguna, da za a rinka kebe wa rumfuna biyar zuwa sama suna kula da masu su da ba su da cikakken ilmin harhada magunguna. Na tabbatar da duk da gwamnati zuwa yanzu ba ta fitar da tsarin yadda tafiyar za ta kasance ba, amma dai na san ba kyauta `yan kungiyar za su yi aikin ba, dole ne duk wadanda za su ci gajiyar shirin za su rinka biyan wasu kudi. 

To, tun da kuwa haka ne, kuma dama `yan kungiyar masu ilmin hada magungunan su  suka matsa wa gwamnati lambar a yi kasuwannin, mai karatu ka ga ke nan tsugunne ba ta kare ba. Mai yiwuwa ma sanin hakan ya sanya Ministan Lafiyar ya yi kira ga `yan kasuwar magunguna na da Aba da lallai su hada kai.

Kazalika, samar da ingantattun ayyuykan kiwon lafiya da ayyukan yi, musamman tsakanin matasan kasar nan za su yi matukar rage masu ta`ammali da miyagun kwayoyi a kasar nan, baya ga killace masu hada-hadar magunguna a wuri daya.