✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gidauniyar Zakka Ta Shirya Wa Marayu Buda-baki A Gombe

'Ya'yan jami'an gidauniyar da suka sha ruwa da marayun sun yi ta wasa tare suna hira da juna bayan shan ruwan

Gidauniyar Zakah da Wakafi a Jihar Gombe ta shirya buda-baki tare da marayu domin faranta musu rai a gidan marayu da ke unguwar Tumfure a fadar jihar.

A buda-bakin na musamman da aka yi tare da iyalan jami’an gidauniya, an soya wa marayun kaji an dafa musu shinkafa da shayi, ga kuma ‘ya’yan itatuwa, alfarmar watan Ramadan.

A yayin ziyarar ‘ya’yan jami’an gidauniyar da suka sha ruwa da marayun sun yi ta wasa tare suna hira da juna bayan shan ruwan.

Shan ruwan ya samu halartar manyan jami’an gidauniyar, ciki har da shugabanta, Dokta Abdullahi Abubakar Lamido, da iyalansu da sauran su.

Shugaban gidauniyar, ya ce makasudin ziyarar shan ruwa da marayun shi ne domin tuna musu cewa wata rana wasu mutane irin hakan za su kula da su a rayuwa kuma za a samu masu taimaka musu a cikin su.

Dokta Lamido, ya ce an kafa gidauniyar ne dan raba zakka da wakafi da kuma taimaka wa marasa galihu da ke cikin al’umma ta kowacce hanya.

Daga nan sai ya yi kira ga masu hannu da shuni da su hada kai da gidauniyar wajen taimaka wa marayu da kuma aike wa da zakkarsu inda ta dace idan suka fitar.