A ranar Talata ce Gidauniyar Tallafa wa Wadanda suka Hadu da Bala’i (bSF), ta raba kayayyakin noma ga manoma fiye da 500 a garin Kukawa da ke Jihar Borno, a wani yunkuri na inganta noman rani a yankin. Babban Daraktan Gidauniyar bSF Farfesa Sunday Ochoche, ya bayyana haka a garin Kukawa da ke karamar Hukumar Baga, lokacin da bikin raba kayayyakin.
Onche ya ce wannan wani yunkuri ne na tallafa wa al’ummar yankin da bala’in Boko Haram ya shafa. Ya ce an zabo kimanin gidaje 1,300 ne daga garuruwan Kukawa da Hawul da Konduga don cin gajiyar shirin. Ya ce wadanda suka ci gajiyar tallafin an ba su kayayyakin da suka hada da irin shuka da takin zamani da magungunan kashe kwari da makunsan yin feshi da injunan ban-ruwa don yin noman rani.
Babban Daraktan ya kara da cewa, gidauniyar ta taimaka wa jama’a da dama a baya a bangaren ilimi, ta hanyar samar musu da litattafan karatu da rubutu da kuma taimaka wa marayu da kuma inganta tunanin mata da yaran da aka kashe iyayensu.
Sannan asusun yana tallafawa a bangaren koyar da kananan sana’o’i da yin sababbin gine-gine a wuraren da aka rusa ko aka kona da taimaka wa wadanda ba su da lafiya da magunguna da sauransu.
Farfesa Ochoche ya ce “Mun gyara gidajen da aka rusa a garuruwan Bama da Kaga da Konduga da sauransu. Sannan mun tallafa wa mata masu yawa a yankin Chibok da Jere da kuma Baga. Hasali ma kwanan nan muka raba kayayyakin karatu da rubutu a garin Kaga. A yau mun zo ne mu kaddamar da shirin noman rani a wannan yanki.
Don haka muna kira ga wadanda suka samu nasarar shiga cikin wannan shiri da su yi wa Allah su koma garin Kukawa su yi noman rani. Zaman da kuke yi a sansanin ’yan gudun hijira ba ya da amfani don zama ne kamar na mabarata da a kowane lokaci kuna jira ne jama’a su kawo muku tallafin abinci da sauran kayayyakin more rayuwa inda a wasu lokuta abin ba kasafai yake kosar da ku ba. Don haka ina kira gare ku, ku koma gidajenku na asali ku rungumi harkar noman rani, hakan zai samar muku da isasshen abinci da kudin shiga da za ku tafiyar da harkokinku da na iyalinku ba tare da wata matsala ba.”
A jawabin Gwamna Kashim Shettima na Jihar Borno wanda ya samu wakilcin Kwamishinan Aikin Gona na Jihar, Alhaji Muhammad Dilli, ya ce wannan tallafi da Asusun bSF ya bayar ko shakka babu zai bunkasa rayuwar al’ummar yankin ta hanyar rungumar noman rani.
Ya ce gwamnatin jihar ta sayo kayayyakin noma na biliyoyin Naira don raba su ga manoma. Ya ce a kan haka ne gwamnati ta bullo da shirin bunkasa noman tumatur da na shinkafa a garin Kukawa. Ya ce gwamnati ta sayo taraktocin noma kimanin dubu 1 kuma za ta raba su ga manoman da ke kananan hukumomi 27 da ke jihar.
Kimanin mutum dubu 80 da aka raba su da muhallinsu ne suka koma gidajensu sakamakon dawowar zaman lafiya.