Wata gidauniya mai rajin habaka harkar ilimin ’ya’ya mata a jihar Yobe, Hausari female Education support Foundation, za ta saka yara mata 150 makarantun boko kyauta a jihar.
Shugabar gidauniyar, Hajiya Hafsatu Alhaji Ado, ta ce za su ba da tallafin ne a kokarinsu na mara wa aniyar gwamnatin jihar baya wajen inganta ilimim ’ya’ya mata.
- Jirgin saman Ukraine da ke dauke da makamai ya yi hatsari a Girka
- Amfanin ganyen ‘aloe vera’ wajen gyara jiki
Ta bayyana hakan ne a lokacin da take zantawa da wakilinmu a Gombe ranar Lahadi, inda ta ce ciyar da ilimin ’ya’ya mata gaba ne makasudin kafa gidauniyar tasu.
Hajiya Hafsatu ta ce gidauniyar sabuwa ce da aka kirkire ta da manufar yin koyi da kyawawan manufofin gwamnan jihar, Yobe Mai Mala Buni, wajen rage yawan mata da ba sa zuwa makaranta a jihar.
A cewarta, za ta cim ma wannnan buri ne ta hanyar shigar da yara matan makaranta da kuma ta daukar nauyin mayar da wadanda suka daina zuwa makarantar.
Daga nan Hafsatu Ado ta ce bayan mayar da mata 150 sun koma makaranta, za ta sake mayar da wasu 20 din da suka daina zuwa makaranta tare da daukar cikakken nauyinsu.