Uwargidan Mataimakin Gwamnan Jihar Sakkwato, Hajiya Hafsat Mannir Muhammad Dan’iya, ta kaddamar da shirin soma koyar da matasa maza da mata sana’o’in hannu domin dogaro da kai, a karkashin gidauniyarta.
Hajiya Hafsat Dan’iya ta ce ta kaddamar shirin ne a wani yunkuri na rage wa gwamnati nauyi, ganin komai an bar shi ga gwamnati.
Shirin da aka soma a Karamar Hukumar Kware, zai karade dukkan mazabu 11 da ke yankin. Kuma za a soma da mazabar Gidan Karma, bayan nan za a kara duba yiwuwar fadada shirin a dukkan kananan hukumomin jihar.
A jawabin Hajiya Hasfat a wurin taron ta ce: “Gidauniyar mai suna ‘Gidauniyar Hafsat Mannir Dan’iya’ an kafa ta ce da niyyar fitowa da shirye-shiryen da za su inganta rayuwar mata da kananan yara da maza matasa, don dogaro da kai da kuma samar wa al’umma hanyoyin yaki da talauci. Ta hanyar shirya horo da fito da sababbin hanyoyin sana’o’in da za su sa arzikin mutum ya bunkasa cikin hanzari. Domin a sauya tunanin mata da matasa daga zaman banza da cima-zaune.”
“Mutum 15 muka dauko da za mu soma da su, bayan mun yaye su za a kira wadansu mata 10 da maza biyar daga mazabar Gidan Karma, wadanda za su koyi sana’o’i daban-daban na dogaro da kai. Za a koyar da su a wannan cibiyar da aka bude a garin Kware a karkashin wannan gidauniyar inda mata za a koya musu dinki da sakar tufafi na zamani da yin sabulu da man shafawa. Yayin da maza kuma za a koya musu sana’o’in yin takalma da zai dauke su wata biyu, ana koya musu a cibiyar,” inji ta.
Ta ce bayan sun kammala za su dawo don yin bikin yaye su da ba su jari don ci gaba da yin sana’o’in da suka koya.
Tun farko Matar Gwamnan Jihar Sakkwato, Hajiya Mariya Aminu Waziri Tambuwal, ta gode wa Hajiya Hafsat game da irin wannan namijin aikin da ta fito da shi domin taimakon al’ummarta, inda ta ce abu ne da ya kamata duk wata mai kishin Jihar ta fito da shi domin kara taimakon shiryen-shiryen gwamnati.
Hajiya Mariya, ta bakin wakiliyarta, Kwamishinar Ilimin Kimiyya ta Jihar Dokta Kulu Abubakar, ta ce da za a rika samun mutane masu tunanin taimakon al’umma ga abin da suke da shi da an samu ci gaba fiye da yadda ake ciki yanzu. Ta yi fatar gidauniyar za ta dore da ci gaba da taimakon al’umma.