✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gidauniya za ta karrama Sarki Sanusi da Kwankwaso a Abuja

Gidauniyar Green Heart Impact Foundation ta shirya tsaf domin karrama Mai martaba sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na 2 da tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu…

Gidauniyar Green Heart Impact Foundation ta shirya tsaf domin karrama Mai martaba sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na 2 da tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a Abuja.

Sauran wadanda za a karrama sun hada da Shugaban Hukumar Alhazai ta kasa NAHCON, Barista Abdullahi Mukhtar da matar Gwamnan Jihar Sakkwato Hajiya Mairo Tambuwal da tsohuwar Ministar Harkokin Mata Hajiya Zainab Maina da shugabar shirin Life Program na matan Afirka da Hajiya Erelu Aisha Babangida da dai sauransu.

Gidauniyar GHIF, gidauniya ce mai kokarin taimakon al’umma musamman a harkokin da suka shafi ilimi da kiwon lafiya da tallafawa mata, kamar yadda shugabar gidauniyar Munira Suleiman Tanimu ta ce.

 

A shirin gidauniyar mai taken ‘Books Over Trays’ gidauniyar GHIF yanzu haka ta dauki nauyin karatun sakandirin mata masu talla guda goma a kowace jihad a ke fadin kasar nan, sannan take tallafawa iyayensu.

 

Ya zuwa yanzu, gidauniyar ta horar da mata 52 a jihohi biyar na Borno da Kaduna da Kano da Neja da Sakkwato tare da tallafawa iyayensu 52 da injin nika da keken dinki da jari domin su fara sana’a.

 

Hajiya Munira ta ce, “Taron karramar zai taimaka mana wajen fadakar da dumbin mutane harkokin Gidauniyar GHIF da nasarorin da suka samu, sannan kuma su kara neman hadin kai da masu ruwa da tsaki wajen taimakon mata da tallafawa iyayensu kamar yadda muka fara tun bara.”