Gidauniyar Fatima Paga Foundation da ke garin Damaturu, babban birnin Jihar Yobe ta shirya aikin ciyar da masu azumi mutum 170 a kowacce rana.
Shugabar gidauniyar, Hajiya Fatima Muhammad Paga, ta ce ta gaji wannan aikin ne daga mahaifinta wanda ya shafe shekaru yana yi.
- Ta’addanci: Pantami ya nesanta kansa da kalamansa na baya kan Al-Ka’ida da Taliban
- Abin da ya sa muka kama gandaye 11 a Kano – Hisbah
Ta ce tun bayan rasuwarsa, mahaifiyarta ta dora daga inda ya tsaya sannan ita kuma yanzu shekara biyu ta kafa gidauniyar domin ci gaba da wannan aiki da kudinta, in banda a bana da ta nemi jama’a su sa tallafin su dan haduwa cikin ladan.
“Na kwadaitu da wa’azin malamai ne a kan ladan ciyarwa musamman ma a wata mai albarka na Ramadan; ga ladan azumi, ga ladan ciyarwa,” inji Fatima.
Tace ta samu tallafi daga wasu mutane hudu wadanda ba su amince a bayyana sunansu ba, sannan ita kuma da ma ta yi nata tanadin.
Gidauniyar dai ta ware wurare hudu da take kai abincin bude-bakin na kunu da shinkafa dafa-duka da nama.
Wuraren dai sun hada da Masallacin Zanna Zakariya da Masallacin Zanna Zakariya da ke layin B da rukunin shagunan Family Support a Damaturu sai Tsangayar Malam Musa da ke Nayinawa a cikin garin Damaturu.
Gidauniyar dai ta fara wannan ciyarwar ne tun a ranar azumin farko, yayin da masu amfana suke jinjina mata tare da yin kira ga saura jama’a su yi koyi da ita.