✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gidan tarihin Birtaniya ya ba da $4m don gina gidan tarihi a Edo

Gwamnan Edo, Godwin Obaseki ya ce gidan tarihi na Ingila ya bayar da gudunmuwar Dal miliyan hudu don gina gidan tarihi na Yammacin Afirka a…

Gwamnan Edo, Godwin Obaseki ya ce gidan tarihi na Ingila ya bayar da gudunmuwar Dal miliyan hudu don gina gidan tarihi na Yammacin Afirka a jihar (EMOWAA).

Obaseki ya bayyana shirin gwamnatinsa na gina EMOWAA ne yayin taron zuba jari na Alaghodaro karo na hudu da aka gudanar a jihar ranar Juma’a.

Gwamnan ya ce “Muna mika godiyarmu ga gidan tarihi na Birtaniya saboda gudunmawar da ya ba mu ta Dala miliyan hudu don gina gidan tarihi”.

Ya ce gwamnatinsa ta himmatu ainun wajen ganin ta farfado da fasahohi da al’adun jama’ar Jihar Edo ta yadda jihar za ta zama ta musanman a Najeriya.

A nasa jawabin, shugaban taron, Asue Ighodaro ya ce taron zai ba masana’antun gwamnati da masu zaman kansu da kungiyoyin sa kai da shugabannin gargajiya na jihar damar tattaunawa don lalubo sabbin hanyoyin bunkasa tattalin arziki jihar.