A ranar 10 ga watan Yulin bana Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, ya sake ayyana gidan tarihi na ‘Hagia Sophia’ a matsayin masallacin Juma’a.
Shugaban ya yi hakan ne bayan wata babbar kotu a kasar ta yanke hukuncin cewa mayar da ginin da tsohuwar gwamnatin kasar ta yi a matsayin gidan tarihi shekaru 86 da suka gabata ya saba doka.
Erdogan fitar da sanarwa jim kadan da yanke hukuncin da kotunb5.
“An yanke sha’warar damka sabon masallacin ga hukumar harkokin addini ta qasa, sannan ta bude shi ga masu ibada,” a cewar Erdogan.
Juma’a 24 ga watan Yuli Erdogan, ya jagoranci tawagar ministocinsa wajen sake bude masallacin inda manyan malaman kasar suka karatan wasu daga cikin ayoyin Al-kur’ani Mai girma wanda shi ma Erdogan, ya karanto ayoyi daga cikin Suratul Bakara da Fatiha.
Dubban masallata sun hallarci sallar Juma’a a babban ginin na Hagia, shekara 86 rabon da a yi haka a Hagia Sophia.
Yaushe aka gina Hagia Sopia?
An kammala ginin Hagia Sopia, a lokacin Sarki Justinian I. Daya daga cikin sarakunan Daular Romawa ta (Byzantine) a wadda take Gabashin Turai, a karni na biyar.
An shafe shekara 5 ana gina wajen bautar daga shekarar 532 zuwa 537, wanda a lokacin shi ne ginin da ya fi kowane girma da kyau ya duniya.
Wanda ya yi zayyanar ginin shi ne Isodore wanda ya fito daga Miletus.
An gina shi a matsayin wajen bautar Kiristoci masu bin darikar Orthodox.
Ginin ya shafe fiye da shekara 900 a matsayin Cocin Daular Rumawa ta Byzantine kafin daga bisani ya shafe fiye da shekara 500 a matsayin Masallaci.
Dawowarsa Masallaci:
Bayan faduwar babban birnin Constantinople (Istanbul) a hannun mayakan Daular Usmaniyya (Ottoman) a shekarar 1453 karkashin jagorancin Fatih Sultan Mehmet II, daga baya aka mai da Cocin Hagia Sopia masallaci.
Zamtowarsa gidan tarihi:
Bayan rushewar Daular Usmaniyya, wanda ya jagoranci kafa Kasar Turkiyya ta yau, Mustafa Kemal Ataturk, ya mayar da ginin Masallacin a matsayin gidan tarihi.
Ya yi hakan ne kasancewarsa wanda ya nesanta gwamnatinsa daga bin tsarin shari’ar Musulunci, a shekarar 1935.
Ya kuma ba da umarnin cire shimfidun da ke cikin masallacin.
Martanin kashen duniya da shugabannin addinai:
Kasar Girka:
Gwamantin kasar Girka ta ce matakin da Turkiyya ta dauka na mayar da Hagia Sopia a matsayin masallaci, ya jifa duniya cikin rudani.
Fadar ta ce abin ya fi wa Girka illa sama da duk wata kasa a duniya kasancewar kusan cinmu da wajen.
Gwamnatin Girka a birnin Athens tana neman hadinkan kasashen duniya domin a kakaba wa Turkiyya takunkumi a kan a bin da ta aikata.
Firai ministan Girka Nikos Dendias ya ce, Erdogan ya fito karara ya bayyana aniyarsa ta sake farfado da Daular Usmaniyya.
Amurka:
Mai magana da yawun fadar Amurka Morgan Ortagus, ya ce “ba mu ji dadin abin da ya faru da gwamnatin Turkiyya ta yi na mayar da Hagia zuwa masallaci ba, muna kira ga gwamnati da ta bar kofa a bude ga masu ziyara ba tare da wani tarnaki ba,” inji shi.
Rasha:
Kakakin Fadar Kremlin Dmitry Peskov, ya ce mayar da Hagia Sopia Masallaci ba zai bata dangantakarsu da kasar Turkiyya ba, dominb matakin hurumin kasar Turkiyya ne.
Ya ce, “da muna sayen tikiti mai tsada kafin mu shiga Hagia amma a yanzu zai zama kyauta ga kowa.
Don haka masu yawon bude ido sune za su yi nasara,” inji shi.
Fafaroma:
Ya bayyana matakin na Turkiyya a matsayin wani al’amari ‘maikkuna’.
Hakan ya biyo bayan suka da fadar Fafaroman ta sha daga ɓangarorin da zargin Fadar Fafaroma da krashin cewa komai a kan al’amarin.
Sheikh Imran Hosain:
Wani malamin addinin Musulunci dan kasar Trinidad, ya bayyana al’amarin da abin kunya da gwamnatin Turkiyya ta jawowa Musulunci a duniya.
Ya ce tun da farko wadanda suka jagoranci yakin da aka hambarar da Daular Byzantine ba su yi jihadi a kan gaskiya ba, kuma mayar da Hagia Sopia zuwa masallaci kuskure ne.
Dakta Zakir Naik:
Malamin addinin musulunci dan kasar Indiya, ya bayyana mayar da Hagia Sopia, da ce wa bai saba ka’ida ba, duba da yadda tarihi ya nuna Fatih Sultan Mehmet II, bayan da ya ci birnin Constantinople da yaki, ya bukaci shugabbanin wannan coci da su sayar masa kuma suka amince suka sayar da wajen bautar ga Sultan, kana daga bisani ya mayar da shi masallaci.
Malamin ya ce ba kamar yadda wasu suke fada ba wai an kwace cocin ne aka mayar da shi masallaci da karfi a wancan lokaci.
Shin an taba mayar da masallaci coci ko wurin bauta?
A 2019 wata kotu a kasar Indiya ta mayar da masallacin Babri, da ake rigima a kai a Arewacin Indiya wajen bautar addinin Hindu.
A hukuncin kotun ta bayyana cewa asali wajen bautar Hindu ne Musulmai suka kwace a shekarar 1592 suka mayar da shi masallaci.
Kotun ta ba da umarnin a bai wa Musulmai wani wajen na daban.
Masallacin Cordoba:
Yana daya daga cikin masallatan da Daular Musulunci ta Andalusiya ta gina a karni na 15 wanda ya zama coci a tarihi.
Masallacin Granada da ke Sifaniya wanda a tarihi ya zama coci sama da shekara 500 da suka gabata.
Manufar Turkiyya:
Masu sharhi sun yi bayanai mabanbanta a dangane da mayar da Hagia Sopia masallaci da Shugaban Turkiyya ya yi, a matsayin kokarin dawo da Daular Usmaniyya wacce ita ce daula ta karshe da Musulmai suka rike.
Daular ta hada da wasu kasashen Larabawa ciki har da garin Makka da Madina da wasu kasashe a yankin Afirka, kafin daular da rushe bayan yakin duniya na farko.
Erdogan wanda ya shafe shekara 17 a kan mulkin kasar Turkiyya, ya kawo sauye-sauye masu yawa ciki har da dawo da kasar a kan manufofin addinin musulinci da kuma sake samun karfin fada a ji a tsakanin kasashen Musulmai.
Turkiyya ta kara fadada rundunar sojinta da kuma gabatar da ayyukan agaji a wasu kasashe kamar kasar Somaliya da kuma nuna kwanji a kasar Libiya wanda ta kai su ga kokarin murkushe ’yan tawayen kasar da kuma tsoma baki a kan duk wani abin da ya shafi Gabas ta tsakiya.
Turkiyya tana daukar kanta a matsayin jagora ga kasahen Musulmai duk da ba ta ga maciji da wasu kasashen Larabawa.