✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gidan rediyon CITAD da VOA Hausa sun kulla yarjejeniyar aiki tare

VOA Hausa da CITAD za su yi aiki tare don bunkasa ayyukansu.

Gidan rediyon Cibiyar Yada Fasahar Sadarwa da Ci Gaba (CITAD) da ke yada shirye-shiryensa a shafukan Intanet ya kulla yarjejeniyar aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA).

Ana sa ran yarjejniyar ta karfafa aikin jarida don cimma nasarori a shirye-shirye da kafar ke watsawa.

Sanarwar yarjejeniyar aikin na kunshe ne cikin wata takarda da wakilin gidan rediyon mai kula da huldar kasuwanci na Sashen Hausa na VOA da ke Najeriya, Malam Sani Mohammed ya sanya wa hannu.

A cewar sanarwar, daga yanzu gidan rediyon na CITAD zai rika yada shirye-shiryen da VOA Hausa ke gabatarwa tare da sanya shi a shafukansu.

Kazalika, sanarwar ta ce daga yanzu VOA Hausa za ta rika gayyatar ma’aikatan rediyon CITAD, domin ba su horo na musamman a kan harkokin yada labarai.

Da ya ke jawabi a kan dangantakar shugaban gidan rediyon na CITAD, jami’in yada labarai na kungiyar, Ali Sabo, ya ce dukkan bangarorin biyu za su amfana da dangantakar, musamman idan aka yi la’akari da yadda zamani ya zo da sauyi a harkar yada labarai.

Ali, ya kuma ce a zamanin da hanyoyin sadarwa na zamani irin su Intanet da wayoyin tafi da gidanka ke samun karbuwa tsakanin al’umma, hakan zai samar da kafofin yada labarai na Intanet, kama daga kan rediyo, jaridu da ma gidajen talabijin, musamman ta hanyar amfani da Intanet wajen yada shirye-shiryensu.