Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati a Najeriya (EFCC) ta mika wa gwamnatin jihar Legas wani katafaren gidan tsohuwar ministar albarkatun man fetur, Diezani Allison-Madueke, domin a mayar da shi cibiyar killace majinyata cutar coronavirus.
A shekarar 2017 ne Babbar Kotun Tarayya da ke zama a Legas ta mallaka wa gwamnatin tarayya ginin mai rukunin gidaje shida masu daki uku da rumfa ko wannen su, da kuma bangaren yara maza (boys quarters), bayan da hukumar EFCC ta kwace shi daga hannun tsohuwar ministar.
A lokacin da yake mika gidan ga gwamnan Legas ranar juma’a, shugaban hukumar EFFC shiyar jihar Legas, Muhammadu Rabo, ya ce matakin da suka dauka kadan ne daga cikin kokarin da hukumar ke yi domin dakile yaduwar annobar COVID-19.
Ya kara da cewa hukumar a shirye ta ke a ko wanne lokaci domin ba da gudunmawarta wajen hana yaduwar cutar.
“A shirye muke mu ci gaba da ba da gudubmawarmu, don haka a duk lokacin da gwamnatin Legas ke bukatar wani abu daga gare mu, ta sanar da mu”, inji shi.
A nasa bangaren, gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, yabawa hukumar ta EFCC ya yi, yana cewa abin alfahari ne duba da yadda gwamnatin tarayya ke hadin gwiwa da gwamnatin Legas wajen tunkarar annobar a Jihar.
Mista Sanwo-Olu ya bai wa hukumar ta EFCC tabbacin aiki da gidan yadda ya dace.
“Rashin wadatattun cibiyoyin killace masu jinyar cutar COVID-19 na cikin manyan kalubalen da muke fuskanta, don haka wannan gudunmawa ta EFCC za ta yi tasiri kwarai a kokarin mu na hana yaduwar cutar”, inji gwamnan.
Hukumar EFCC ta kwace tarin kadarori na tsohuwar minista Allison Madueke, wadanda suka hada da gidajen alfarma da tarin gwalagwalai da sauran kayan ado da na kawa wadanda kotu ta mallaka wa gwamnatin tarayyar Najeriya.