Masallacin Ka’aba, Makka
Allahu Akbar! Ya bayin Allah! Shin wannan dabi’ar Mumini ne ya aikata irin wadannan munanan abubuwa ga dan uwansa? Ku tuna kowane mutum yana nuna so yana nuna ki, yana yarda, yana fushi, yana jibinta, yana adawa, sai dai mai hankali ba ya jibintar wani ba kaidi, ko ya ki wani mutum gaba daya, sai dai ya so wani abu daga gare shi, ya ki wani abu daga gare, ya so wata dabi’a daga gare shi, ya yi watsi da wata. Mai hankali shi ne yake son masoyinsa da sauki, don yana iya zama makiyinsa wata rana, ya ki makiyinsa da sauki don yana iya zama masoyinsa wata rana. Kuma hankali da addini sun nuna muku cewa kada ku mayar da aibobin wanda kuke so su zama kyawawan ayyuka, har ya zamo kun dauka ba sa da wani sharri gaba daya. “Ya ku wadanda suka yi imani! Ku kasance masu tsayin daka domin Allah, masu shaida da adalci. Kada kiyayya da wasu mutane ta dauke ku a kan ba za ku yi adalci ba. Ku yi adalci. Shi ne mafi kusa da takawa.” (k: 5:8).
Ya ku ’yan uwa! Abin yakan fi muni da zama abin kyama da girman zunubi, idan aka ce giba tana fitowa ne daga mutanen da suke da dangantaka da ilimi da himmar kawo gyara a tsakanin mutane, mutanen da suke adontuwa da alamar zuhudu da kyamar duniya, amma a ce sun hada gibarsu a tsakanin tsarkake kansu da sukar wasunsu. Ku leka abin da Imam Al-Gazali ya rubuta a littafinsa Al-Ihya’u, ko Ibn kudama Almukaddasi a Mukhtasar Manhaj ko Ibn Hajri Alhaisimi a Zawajir, inda suka yi magana a kan nau’o’in wadannan mutane.
Allahu Akbar! Ya ’yan uwa wani magabacin kwarai ya ce, “Mun riski mutanen kirki ba su ganin ibada ta takaita a kan Azumi da Sallah, a’a har ma da kamewa daga kutsawa cikin mutuncin mutane. Don haka ka yi zaton alheri ga ’yan uwanka da makusantanka, kada ka saurari wanda rabonsa ya karanta a wurin Allah. Ka ambaci dan uwanka idan ba ya nan da abin da kake son a ambace ka da shi, ka yi masa afuwa cikin abin da kake son a yi maka afuwa. An ce wa wani bawan Allah: “Hakika wane ya bata ka, har muka tausaya maka. Sai ya ce, shi ya kamata ku tausaya masa.” Sannan wani mutum ya ce wa Alhasan, “Na samu labarin cewa kana gibata. Sai ya ce: “Ba ka kai matsayin da zan so a debi kyawawan ayyukana a ba ka ba!”
Don haka ku ji tsoron Allah, Allah Ya jikan wanda abin da yake kansa ya hana shi duban na mutane, Allah Ya jikan wanda ya yi riko da koyarwar Littafin Ubangijinsa ya koma ga Majibincinsa da zuciya yaradajjiya da harshe mai gaskatawa, ya so wa ’yan uwansa abu mai kyau. “Ya Ubangijinmu! Ka yi gafara a gare mu, da kuma ’yan uwanmu wadanda suka riga mu yin imani, kada Ka sanya wani kulli a zukatanmu ga wadanda suka yi imani. Ya Ubangijinmu! Lallai Kai ne Mai tausayi, Mai jinkai.” (k: 59:10).
Huduba ta biyu:
Godiya ta tabbata ga Allah Ma’abucin Al’arshi Mai girma. Mai aikata abin da Ya yi nufi, Ya kewaye komai da iliminSa, kuma Shi Yana halarce a kan komai. “Babu abin da (bawa) yake furtawa face a kansa akwai wani mai tsaro mai karfi.” Na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, ba Ya da abokin tarayya, kuma Shi ne Mafi kusanci ga mutum daga jijiyar wuyarsa. Kuma na shaida lallai Shugabanmu Annabi Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa, ya yada ilimin tauhidi, Allah Ya kara tsira da aminci da albarka a gare shi da alayensa da sahabbansa da wadanda suka biyo su da kyautatawa cikin bayin kirki da aminci aminci mai yawa.
Bayan haka, ya ku Musulmi! Daga cikin mafiya hadarin abin da ma’abuta ilimi suka ambata na daga aibobin giba da take darsuwa a zuciya, sun ce akwai mummunan zato ga Musulmi. Zato kuwa shi ne abin da rai da zuciya suke karkata gare shi, amma darsuwar zancen zucci kawai ana afuwa a kansa. Bai dace ba ka yi mummunan zato ga dan uwanka, duk lokacin da mummunan zato ga Musulmi ya darsu a zuciyarka, wajibi ne ka kiyaye shi tare da yi masa addu’ar alheri. Wannan yana fusata Shaidan ya tunkude shi daga gare ka. Idan ka tabbatar da kuskure daga Musulmi, to, ka yi masa nasiha, kada ka kunyata shi. Mummunan zato yana jawo binciken laifi da bin gazawar mutum, zuciya kuwa idan aka kyale ta, ba ta cika tsayawa kan zato ba, takan nemi sanin hakikanin abu, don haka sai ta shagaltu da binciken laifi, wannan kuwa abin da shari’a ta hana ne, domin yana jagoranci zuwa ga keta suturar Musulmi.
Ya ku ’yan uwa! Mai sauraren giba abokin tarayya ne ga mai yin gibar, ba zai tsira daga zunubi ba, har sai ya bayyana kin sa ga hakan da harshensa, idan ba zai iya ba, to, ya ki da zuciyarsa. Idan yana da ikon tashi daga wurin, to ya tashi, ko ya yanke maganar da wata maganar.
Ka guje -tare da neman tsarin Allah- daga wanda zai saurari giba ya rika nuna sha’awa don ya kara wa mai gibar nishadi. Domin malamanmu Allah Ya rahamshe su sun ce: “Gaskata giba, giba ce, mai shiru kanta abokin tarayyar mai giba ne.” Ba ka ganin mai karfin imani da rashin tsoro shi ne wanda yake kin a yi gibar wani a wurin zamansa, kuma yake kin kunnesa ya ji an aibata dan uwansa Musulmi? Ibn Mubarak (Allah Ya yi masa rahama) ya ce, “Ka guji giba kamar yadda za ka guje wa zaki.” Ina za a samu Mumini mai karfin imani da zai zauna da mai giba? Maimun bin Sayyah ya kasance wani ba ya gibar wani a wurinsa face ya hane shi, idan kuma ya ki sai ya tashi ya bar wurin.
Ya bawan Allah! Ko wadanne mutane suna da al’aura da aibobi da kura-kurai da gazawa da suke bukatar a suturce musu, don haka kada ka dauka ka san abin da wani bai sani ba, ko ka riski abin da wani ya kasa. Shin aibinka ya shagaltar da kai daga ganin aibobin mutane? Ko ka bi hanyar nasiha ka kauce wa hanyar kunyatawa? Ko ka san wanda ya yi magana kan abin da bai shafe shi ba, ya kauce wa gaskiya?
Ka kiyaye hakkin dan uwanka, ka tsare mutuncinsa, ya zo cikin Hadisi cewa “Wanda ya kare mutuncin dan uwansa alhali ba ya nan, hakki ne a kan Allah Ya ’yanta shi daga wuta.” Kuma “Duk wanda ya kasance yana da wani zalunci na dan uwansa, ya alla na bangaren mutunci ko dukiya, to, ya hanzarta biyansa tun kafin ranar da ba Dinari da Dirhami ta zo, in da za a debi kyawawan ayyukansa a biya wancan, idan suka kare, sai a debo zunubban wancan a kara a kan nasa zunubban sannan a tunkuda shi a wuta!
Ku ji tsoron Allah, Allah Ya yi muku rahama, kuma ku gaggauta tuba da neman yafiya da kubuta daga ’yan uwanku. Ku guji kulli da hasada da keta da jin haushin juna a tsakaninku. Allh Ya yi mana gafara.