✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Giba da illarta ga zamantakewar Musulmi (1)

Huduba ta farkoGodiya ta tabbata ga Allah, muna gode maSa, muna neman gafararSa muna neman tsarinSa daga sharrin kawunanmu da munanan ayyukanmu, wanda Allah Ya…

Huduba ta farko
Godiya ta tabbata ga Allah, muna gode maSa, muna neman gafararSa muna neman tsarinSa daga sharrin kawunanmu da munanan ayyukanmu, wanda Allah Ya shiryar babu mai batar da shi, wanda kuma Ya batar babu mai shiryar da shi. Mun shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kadai ba Ya da abokin tarayya, kuma mun shaida Shugabanmu Annabi++ Muahmmad bawanSa ne kuma ManzonSa. Allah Ya kara tsira da amince a gare shi da alayensa da sahabbansa da masu bin su da kyautatawa har zuwa Ranar karshe.
Bayan haka, ina yi mana wasiyya mu yi wa Allah Madaukaki takawa, wanda ya yi maSa takawa (Allah) Ya isar masa, wanda ya ji tsoron mutane ba su isar masa. Ina yi mana wasiyya da takawa, wadda (Allah) ba Ya karbar waninta, kuma ba Ya jinkan kowa sai ma’abutanta, ba Ya bayar da lada sai a kanta, masu wa’aztuwa da ita suna da yawa, amma masu aiki da ita kalilan ne, Allah Ya sanya mu cikin masu takawa.
Ya ku Musulmi! Addinin Allah ya cika ya kammala, ya kunshi akida da shari’a da tauhidi da ibada da mu’amala da ada, yana zance da hankali da zuciya da jiki da rai a cikin al’amuran da suka shafi shari’a da halaye da tarbiyya, addini daga Ubangijinmu yana tsara dokoki da tsara rayuwa ga Musulmi mai mutunci da tsarki na zahiri da badini, Musulmi mai kubutacciyar zuciya, mai kame harshe, mai da’a ga Ubangijinsa mai halin kirki ga jama’a. Mai kokarin tsare mutuncinsa da kin bin son rai. “Ya ku wadanda suka yi imani! Ku nisanci abu mai yawa na zato. Lallai sashin zato zunubi ne. Kuma kada ku yi rahoto, (binckar laifin mutane).” (k: 49:12).
Musulunci addini ne na gaskiya da hukunce- hukuncen addini suke ta’allaka da shi tare da tsarkake zukata, al’amura su rika gudana bisa ma’aunin gargadi. Addinin da ke rainon jama’a masu addini da gudun abin da aka haramta, masu kamewa daga giba da halartar wurin da ake gibar, ba su yin mummunan zato ga kowa, kuma ba su neman bankado al’aurorin mutane.
Ya ku ’yan uwa! daya daga cikin dabi’un da wannan addini ya tsayu wajen yaka, yaki na sosai saboda illarsa a tsakanin al’umma da lalata al’amura da jawo rashin mutunci da raunana addini da zubar da mutuncin mutane, kuma daya daga cikin manyan kaba’irai, masu jawo ukuba da mai aikata su ko mai yarda da su da mai saurarensu suke da zunubi, shi ne giba, wato ka ambaci laifin mutum a bayansa, ko ka ambaci dan uwanka da abin da ba ya so, ya alla yana da wannan abin da ka fada ko a’a. Haka Manzonmu Muhammad (SAW) ya bayyana.
Ubangijinku Yana cewa: “Kuma kada sashinku ya yi gibar sashi. Shin dayanku yana son ya ci naman dan uwansa yana matacce? To, ku ki shi (cin naman). Kuma ku bi Allah da takawa. Lallai Allah Mai karbar tuba ne, Mai jin kai.” (k:49:12).
Ya ku Musulmi! Lallai jininku da dukiyarku da mutuncinku haramun ne a tsakaninku. Giba tana da sunaye uku cikin Littafin Allah, wato giba da kage da kirkirar karya. Idan abin da aka fada kan mutum daidai ne, shi ne giba, idan kuma ka fadi abin da ya zo maka, to ya zama kage, idan kuma ba haka lamarin yake ba, to, ya zama keren karya, haka ma’abuta ilimi suka bayyana. Giba ta kunshi duk abin da yake nufin batunci ya alla ta magana ko yafuce da zunde ko a rubuce, domin alkalami shi ma harshe ne.
Giba tana iya zama ta hanyar nakasa mutum kan addininsa ko halinsa ko dabi’rsa ko dangantakarsa ko nasabarsa, kuma duk wanda ya aibata sana’a ba shakka, ya aibata ma’abucinta ne.
Ku saurari yadda Annabinku Muhammad (SAW), yake kiran wadanda aka jarabta da wannan cuta mai halakarwa: “Ya wanda ya yi imani da harshensa, amma imani bai shiga zuciyarsa ba, kada ku yi gibar Musulmi, kada ku bi al’aurorinsu, domin duk wanda ya bi al’aurar dan uwansa, Allah zai bi al’aurarsa, wanda kuwa Allah Ya bi al’aurarsa, zai kunyata shi koda a tsakiyar gidansa ne kuwa.”
Alhassan (Allah Ya yi masa rahama) ya ce, “Wallahi giba ta fi saurin cinye addinin mutum fiye da yadda tsutsa ke cin naman mutumin da ya mutu.”
Ka ji mamakin mutumin da ke jingina kansa da ma’abuta gaskiya, ta yaya zai rika aikata giba, alhali ya san wanda aka jarabce shi da giba yana da karkatacciya kuma bakar zuciya wadda ta ginu a kan kin mutane da kin alheri, ba ya damuwa da nasa laifin kamar yadda yake damuwa da laifin waninsa! Hutunsa da natsuwarsa ya ga ni’ima ta gushe daga waninsa, ya ga kullum bala’i yana samunsa, abin da yake faranta masa rai ya ga dan uwansa bai samu wani alheri ba, ya ga masifa tana sauka masa a kai-a kai! Fushinsa da bacin ransa ya ga alheri ya same ka, ko a ce ka dace ko arziki ya zo maka cikin sauki, ko ya ga wani alheri yana biyowa ta hannunka. Shin dabi’ar Mumini ne wannan? Shin Mumini zai so cutar da dan uwansa kuma a ce ba ya son ’yan uwantakar imani ta darsu a zuciyarsa? “Shin dayanku na son ya ci naman dan uwansa yana matacce?” (k:49:12).
Ma’abucin giba mutum ne mai zakin baki, idonsa a bushe, ba ya da imanin da zai hana shi yin giba, ba ya da muru’ar da za ta ingiza shi ga kyawawan halaye, idan ya samu abokin giba sai dabi’arsa ta koma kamar ta jahilai, ya yi ta sakin magana har ta kai ma’abuta imani su kosa da shi. Zai rika sakin baki a kan shugabanni da malamai da masu kima da ma’abuta matsayi, kai har a kan wawa da jahili a  kowane wurin zama da wurin taro. Magana a wajensa abar sha’awa ce, idan aka dora shi kan sha’anin mutane ya bata al’amarin, idan zai yi magana kan al’amarin addini da ilimi sai ya juya gaskiya har ya zubar da kimarsa. Zai yi ta surutu har mai hankali ya gane cewa ba ya da kaifin hankali da dogon tunani. Mai yawan gardama, yana kutsawa da harshensa cikin addini da siyasa da ilimi da adabi, wannan shi ne sababin tabarbarewar ilimi da bullowar sababbin mazhabobi da rarrabuwar kai a al’amuran addini da harkokin rayuwa. Abin kaico ne a rika amfani da harshe wajen jidali da jayayya da giba da keren-karya da kage.
Mai giba a duk inda ya zauna yakan bata lokacinsa ne wajen bin aibobin mutane da neman kura-kuransu, ba ya jin dadin komai, illa kutsawa cikin mutuncin mutane, mai zunde mai yafuce mai yada annamimanci, bonensa, sannan bonensa! Yana furta maganar da za ta jefa shi a wuta na tafiyar da ta fi nisan da ke tsakanin Gabas da Yamma.
Ya ku Musulmi! Mafi munin wannan da makamantansa da mutum ke aukawa ciki, shi ne gibar ma’abuta al’amuran Musulmi (shugabanni) da ma’abuta ilimi da masu tsare doka da kula da kyautata tarbiyya, mutanen da suke umurni da gyara a tsakanin jama’a. Sai su rika kutsawa cikin mutuncin mutanen kirki masu kima, suna zubar da mutuncinsu da martabarsu suna sukarsu da bata su, suna sukar kyawawan ayyukansu, suna sanya shakku kan matsayinsu da cancantarsu.
Ba za a ambaci wani babba ba, face sun nakasa shi, ko sun zage shi, ba za a bijiro da wani mutumin kirki ba, face sun tuhume shi, suna watsa karya da jirkita abubuwa, suna tuhumar amintattu suna auka wa salihai, suna tayar da fitina suna shuka gaba da kiyayya, suna yanke zumunta suna rarraba kan jama’a, suna rura wutar gaba, suna watsa ma ta fetur, suna watsa tuhumomi iri-iri suna bin aibobi, su ce wannan zololo ne, wancan dan dukwi ne, wannan jahili ne, wancan fasiki ne, wannan mai kazar-kazar ne, wancan kuwa jirgin dankaro ne, idanuwansu suna yafuce, harsunansu suna zunde, wuraren zamansu sharri ne, zama da su cuta ce, aikinsu abin ki ne, maganganunsu ababen kyama ne!