Ghana yi amai ta lashe kan gargadin da ta yi wa ’yan kasarta na zuwa Abuja a bisa fargabar barazanar ta’addanci.
Gwamnatin Ghana ta janye sanarwata tare da bayar da hakuri ga Najeriya ne a wata sanarwa da ta fitar a ranar Alhamis.
- Ghana ta koro ’yan Najeriya 16 kan damfara ta intanet
- Ghana ta zaftare albashin Shugaban Kasa saboda matsin tattalin arziki
Ma’aikatar Harkokin Kasashen Waje ta kasar ta kuma ce, ba ta da masaniyar wata barazana ga ’yan kasar mazauna Najeriya sannan ta nemi afuwa dangane da gargardin, wanda ta ce ba ta ma san da shi ba, duk da cewa da sunanta a ka yi.
Sanarwa ta ce, ’yan Ghana na zaune lafiya da ’yan uwansu ’yan Najeriya, kuma babu wata barazana ga rayuwarsu ko kuma dukiyoyinsu.
A ranar 16 ga watan Nuwamba ne ma’aikatar ta fitar da wata sanarwa da ke gargadin ’yan kasar Ghana da su guji zuwa Abuja, sai idan zuwa birnin ya zama dole.
Sanarwar ta lissafa ta’addanci, da garkuwa da mutane, da sauran matsaloli na tsaro a matsayin hujjar ta yin gargadi.
Vanguard.