✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gerard Piqué na Barcelona zai yi ritaya daga taka leda

Gerard Piqué ya ce zai yi ritaya daga mirza leda kafin karshen watan Nuwamba da muke ciki

Mai tsaron baya na kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Gerard Piqué, ya bayyana aniyarsa ta yin ritaya daga buga wasa kafin karshen watan Nuwamba da muke ciki.

Dan shekara 35 da haihuwa, Gerard ya ce zai yi ritaya ne da zaran an tafi hutun Gasar La liga, gabannin Gasar Kofin Duniya da za a yi a kasar Qatar daga ranar 20 ga watan Nuwamban nan.

“Kwallon kafa ta yi min komai, kungiyar Barcelon ta yi min komai, haka kuma masoyana kun yi min komai,” in ji Gerard.

Ya fadi hakan ne a wani sako da ya sa shafinsa na Twitter a ranar Juma’a.

Mai tsaron gidan ya buga kwallo a gasar La liga takwas da kuma Gasar Zakarun Turai guda uku a tsawon zamansa a kungiyar ta Barcelona.