Jam’iyyar PDP ta ce Shugaba Buhari da ya riga ya gama gazawa a harkokin mulki.
A martaninta ga Shugaba Buhari wanda a ranar Alhamis ya ce ba zai bar ofis a matsayin wanda gaza ba, PDP ta ce kalaman nasa ihu bayan hari ne.
- Kisan Jibiya: Ku dauki makami ku kare kanku —Masari
- ‘Ba zan sauka daga mulki ba har sai na kawo karshen matsalar tsaro’
Sanarwa da ta fitar a ranar Juma’a ta hannun Sakataren Yada Labaranta, Kola Ologbondiyan, ta ce Buhari da jam’iyyarsa ta APC su sani cewa “Borin kunya da kame-kame” ba su fisshe su ba.
A cewarta, Shugaba Buhari da APC sun kasa cika ko daya daga cikin alkawura uku da suka dauka na samar da tsaro da yaki da rashawa da bunkasa tattalin arziki.
Olagbondiyan ya ce “PDP ta yi amanna cewa Shugaba Buhari ya amince da gazawarsa, kuma kokarinsu na wanke APC zai tashi a banza.
“Nan gaba kada APC a takarda za ta koma, za a neme ta a rasa a fagen siyasa, saboda ta nuna kanta a matsayin gurbataccen dandamali wanda ba za a iya ba shi amanar mulki ba a kowane mataki.”
Olagbondiyan ya zargi APC da “lalata dukkannin bangarorin rayuwar al’ummarmu.
“Me Shugaba Buhari da APC zai cewa kan gazawarsu wajen magance matsalar ’yan ta’adda da masu tayar da kayar baya da garkuwa da mutane, da suka addabi al’ummominmu a jihohi daban-daban a fadin kasar nan, duk da dimbin albarkatun da Allah Ya hore wa kasar?
“Ta yaya Shugaba Buhari da shugabannin APC suke iya barci alhali sun san cewa gazawarsu ce ta jefa daruruwan ’yan Najeriya, ciki har da ’yan makaranta cikin mawuyacin hali na masu garkuwa da mutane?
“Buhari ya gaza a matsayin Babban Kwamandan Tsaro saboda ’yan ta’adda na cin karensu babu babbaka, inda yanzu yankuna ke kafa matakan tsaronsu.
“Gwamnoni, har da na jihar Katsina, inda Shugaban Kasa ya fito, Aminu Bello Masari, ke ce wa mutanen da ’yan ta’adda suke kai wa hare-haren su kare kansu.
“Bugu da kari, Fadar Shugaban Kasa ba za ta iya nuna wani muhimmin aikin da ta kirkiro, aka fara shi aka aka kammala shi a cikin shekara shida da suka gabata ba.
“Abin da kawai ta iya shi ne jinginar da makomar al’ummarmu da tarin bashin Naira tiriliyan 33.107 ba tare cikakken tsarin yadda za ta biya ba.
“Mafi munin abin ma shi ne Shugaban yana neman aron karin Naira tiriliyan 5.62, alhali ya san abin da ya rage masa a kan mulki bai kai shekara biyu ba,” inji PDP.
Sakataren Kwamitin Rikon kwarya na APC, Sanata John James Akpanudoedehe da Mataimakin Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar na Kasa, Yekini Nabena ba su amsa kiran waya da sakonnin da aka aiko masu ba, har zuwa lokacin da aka hada wannan rahoton.