✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gaza: Isra’ila ta kashe mutum 195 a sansanin gudun hijira

Kungiyar Hamas ta bayyana cewa Isra'ila ta kashe mutum 195 a sansani Gudun Hijira na Jabaliya da ke Zirin Gaza a cikin kwana biyu

Kungiyar Hamas da ke iko da Zirin Gaza ta bayyana cewa Isra’ila ta kashe mutum 195 a sansani Gudun Hijira na Jabaliya a cikin kwana biyu.

Hamas ta sanar cewa, “wadanda hare-hare biyu da Isra’ila ta kai a sansanin Jabalia ya haura 1,000 ciki har da wadanda da suka rasu da wadanda suka jikkata.”

Sanawar da kungiyar ta fitar ta ce, hare-ahren na ranakun Talata da Laraba sun “yi ajalin mutum 195, wasu 120 sun bace, baya ga wasu 777 da aka jikkata.”

Ma’aikatar lafiya ta Hamas ta bayyana cewa kawo yanzu mutum 8,796 ne suka mutu, yawancinsu mata da kananan yara,  a sakamakon hare-haren Isra’ila.Tun ranar 7 ga watan Oktoba Isra’ila ta fara luguden wuta a ta sama a Zirin Gaza, bayan harin da Hamas ta kai mata, inda ta kashe mutum 1,400 ta yi garkuwa da wasu 230 a Isra’ila.